Tinubu Ya Kirkiro Sabuwar Ma’aikatar Tarayya, Ya Kafa Kwamitin Kiwon Dabbobi

Tinubu Ya Kirkiro Sabuwar Ma’aikatar Tarayya, Ya Kafa Kwamitin Kiwon Dabbobi

  • A wani yunkuri na magance rikici tsakanin makiyaya da manoma, shugaba Bola Tinubu ya kirkiro wata sabuwar ma’aikatar
  • An sanar da kirkirar ma’aikatar ne a yayin kaddamar da kwamitin aiwatar da gyara kan harkokin kiwon dabbobi a fadar shugaban kasa
  • An ce dan komai ya kammala, shugaban kasar zai mikawa majalisar tarayya sunan wanda yake so ya zama ministan sabuwar ma'aikatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin kirkirar sabuwar ma’aikatar tarayya da za a rika kira da 'Ma’aikatar Raya Dabbobi'.

An sanar da kirkirar ma’aikatar ne a yayin kaddamar da kwamitin aiwatar da gyara kan harkokin kiwon dabbobi domin magance rikicin manoma da makiyaya a Abuja.

Kara karanta wannan

Jami'ar Kwara ta kori dalibai 175, an zayyana manyan laifuffukan da suka aikata

Shugaba Tinubu ya kirkiro sabuwar ma'aikatar bunkasa kiwon dabbobi
Tinubu ya kirkiro ma'aikatar bunkasa kiwon dabbobi, ya kafa kwamiti. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Tinubu ya kirkiro ma'aikatar kiwo

Rahoton Channels TV ya nuna cewa shugaban kasar ne zai jagoranci kwamitin, tare da tsohon shugaban hukumar INEC, Attahiru Jega a matsayin mataimakin shugaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari da nufin samar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma tare da tabbatar da tsaro da tattalin arzikin ‘yan Najeriya.

An ruwaito cewa idan komai ya kammala, shugaban kasar zai mikawa majalisar tarayya sunan wanda yake so ya zama ministan sabuwar ma'aikatar.

Tinubu ya amince da kwamiti kan kiwo

Wadanda suka halarci bikin kaddamar da kwamitin sun hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

Sauran sun hada da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da sauran mambobin majalisar zartarwa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A watan Satumbar 2023, Shugaba Tinubu ya amince da kafa wani kwamitin shugaban kasa domin sake fasalin harkar kiwo da kuma magance fadan makiyaya da manoma a kasar.

Kara karanta wannan

Zambar N80bn: Kotu ta yi watsi da bukatar Yahaya Bello na canja wurin shari'arsa da EFCC

A baya ma kungiyar Fulani ta Miyetti Allah (MACBAN) ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya samar da ma’aikatar kiwon dabbobi.

Tinubu ya samu tazarce a ECOWAS

A wani labari na daban, mun bayyana muku yadda Shugaba Tinubu yayi nasarar samun tazarce na mulkin ECOWAS.

An yi taron kungiyar ECOWAS din a Abuja wanda ya samu halartar shugabannin Afrika ta yamma inda suka sake zaben Tinubu don jagorancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.