Samoa: Ƙungiyar Lauyoyi Ta Yi Martani Kan Yarjejeniyar, Ta Fadi Rawar da Ta Taka

Samoa: Ƙungiyar Lauyoyi Ta Yi Martani Kan Yarjejeniyar, Ta Fadi Rawar da Ta Taka

  • Yayin da ake cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa, kungiyar lauyoyi ta NBA ta fayyace gaskiya game da lamarin
  • Shugaban kungiyar, Yakubu Maikyau shi ya bayyana haka inda ya ce kwata-kwata babu batun auren jinsi a yarjejeniyar
  • Maikyau ya ce kafin sanya hannu a yarjejeniyar sai da Ministan Kasafi da tsare-tsare ya bukaci kungiyar ta yi duba kan dokar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar lauyoyi a Najeriya (NBA) ta yi martani kan yarjejeniyar Samoa a kasar.

Kungiyar lauyoyin ta fayyace komai kan zargin sanya hannu a yarjejeniyar da ake cewa akwai amincewa da auren jinsi.

Kungiyar lauyoyi ta yi martani kan yarjejeniyar Samoa
Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA ta bayyana matsayarta kan yarjejeniyar Samoa. Hoto: @officialABAT/@DrDennisOuma.
Asali: Twitter

Kungiyar lauyoyi ta yi magana kan Samoa

Kara karanta wannan

LGBT: Jerin kasashen Afirka da suka sanya hannu a yarjejeniyar Samoa

Shugaban kungiyar, Yakubu Maikyau shi ya bayyana haka a jiya Litinin 8 ga watan Yulin 2024 a Abuja, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maikyau ya ce babu maganar auren jinsi a cikin yarjejeniyar kamar yadda ake yadawa a fadin kasar.

Ya ce Najeriya ba ta amince da auren jinsi ba wanda hakan ya saba dokar kasar da yanzu ake da ita, Punch ta tattaro.

Yakubu ya ce idan da an tilasta Gwamnatin Tarayya amincewa da auren jinsi kafin ba da bashin, da kungiyarsu ba za ta bari ba.

Samoa: Kungiyar NBA ta bayyana matsayarta

"Saboda cire duk wani shakku, yarjejeniyar Samoa ba ta dauke da maganar auren jinsi a cikinta."
"Kafin sanya hannu kan yarjejeniyar, Ministan Kasafi da tsare-tsare ya bukaci kungiyar NBA ta yi duba kan lamarin."
"Na kafa kwamiti na musamman da ke dauke da manyan lauyoyi domin bincikar dokar da kuma ba da shawarin da ya dace."

Kara karanta wannan

Samoa: Malaman Musulunci sun magantu kan yarjejeniyar, sun gargaɗi Majalisar Tarayya

- Yakubu Maikyau

Farfesa Maqari ya magantu kan yarjejeniyar Samoa

Kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci, Farfesa Ibrahim Maqari ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa da ake cece-kuce a Najeriya.

Farfesa Maqari ya shawarci al'umma su yi adalci ga wadanda suke so da ma wadanda basu so kafin yin martani kan abu.

Ya ce tabbas ya yi zama da wadanda suke da masaniya kan lamarin inda suka tabbatar babu maganar auren jinsi a yarjejeniyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.