Tinubu Ya Tura Sakon Jinjina Ga Sheikh Dahiru Bauchi Bayan Cika Shekaru 100
- Babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi yana cigaba da samun sakon barka bisa cika shekaru 100
- Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shiga ciki sahun manyan mutane da suka taya babban shehin malamin murna
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi addu'a da fatan alheri ga Sheikh Dahiru Bauchi bisa matakin shekaru da ya taka a rayuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya taya Sheikh Dahiru Usman Bauchi murnar cika shekaru 100.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa malamin ya yi abin kirki cikin shekaru da ya shafe a duniya.
Legit ta gano haka ne a cikin sakon da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin sadarwa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu: 'Shehi ya ba da gudunmawa'
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya bayar da gudummawa a bangarori da dama a Najeriya.
Bola Tinubu ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa ilimi da tarbiyya a fadin Najeriya.
A bisa haka ne shugaban kasar ya jinjinawa jagoran darikar Tijjaniya bisa kokarin da ya yi na samar da matasa masu ilimi da tarbiyya a Najeriya.
Tinubu ya yi addu'a ga Dahiru Bauchi
A cikin sakon da shugaban kasa ya aika, ya yi addu'a ta musamman ga Sheikh Dahiru Bauchi kan cigaba da samun lafiya, rahoton Daily Trust.
Har ila yau, Bola Tinubu ya roki Allah ya cigaba da ba Sheikh Dahiru Usman Bauchi hikima wajen jagorantar al'umma.
Bincike ya nuna cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekaru 100 a duniya ne a kan lissafin kalandar Musulunci.
Tinubu ya tura sakon ta'aziyya
A wani rahoton, kun ji cewa an shiga jimami bayan rasuwar mahaifiyar Ministar kasuwanci da masana'antu a Najeriya, Dakta Doris Uzoka-Anite.
Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar Victoria Immaculata Uzoka inda ya yi mata addu'o'i na musamman.
Asali: Legit.ng