Gwamnati Ta Janye Harajin Shigo da Kayan Abinci Daga Ketare Domin Kawo Saukin Rayuwa

Gwamnati Ta Janye Harajin Shigo da Kayan Abinci Daga Ketare Domin Kawo Saukin Rayuwa

  • Gwamnatin tarayya ta fara daukar matakin sauko da farashin kayan abinci da su ka yi tashin gwauron zabo a kasuwannin kasar nan
  • Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ya ce an dakatar da harajin wasu nau'in abinci domin saukakawa yan kasa
  • Daga cikin abincin da aka dakatar da harajin su na kwanaki 150 akwai shinkafa da masara da wake da alkama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Gwamnatin tarayya ta amince da shigo da wasu muhimman kayan abinci ta iyakokin kasar nan ba tare da biyan kuɗin haraji ba. Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

Sen. Abubakar Kyari CON
Gwamnati ta dakatar da harajin shinkafa, masara da wake na kwanaki 150 Hoto: Sen. Abubakar Kyari, CON
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an cire harajin nau’ukan kayan abincin irinsu shinkafa da wake da alkama da masara domin rage tsadar kayan abinci.

An dauke harajin abinci na kwanaki 150

Gwamnatin tarayya ta dauki matakin da zai rage tsadar kayan abinci a kasuwannin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya bayyana cewa an dakatar da haraji kan muhimman kayan abinci na kwanaki 150.

The Nation ta wallafa cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da janye harajin domin saukakawa 'yan kasa.

Ministan ya kara da cewa gwamnati za ta shigo da alkama kimanin tan dubu 250 da masara tan dubu 250 da za ta ba wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.

Wannan na zuwa ne bayan an shafe watanni ana shawartar Bola Ahmed Tinubu ya bude iyakokin kasar nan da aka rufe tun a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

An shawarci gwamnati kan bude iyakoki

A wani labarin kun ji cewa hukumar kare hakkin masu sayayya ta kasa ta shawarci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bude iyakokin kasar nan.

Mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi ne ya bayar da shawarar inda ya ce ana sa ran bude iyakokin zai taimaka wajen shigo da abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.