Rikicin Masarauta: An Aika Gargadi ga Kwankwaso da Jam'iyyar NNPP
- Jam'iyyar NNPP da shugabanninta sun samu sabon gargaɗi daga ƙungiyar Progressives Front of Nigeria (ProFN)
- Ƙungiyar ta gargaɗi Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso da NNPP kan ɓata sunan Bola Ahmed Tinubu saboda rikicin masarautar Kano
- Gargaɗin na ƙungiyar na zuwa ne bayan shugaban NNPP na jihar Kano ya yiwa Tinubu barazana kan rikicin masarautar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ƙungiyar Progressive Front of Nigeria (ProFN) ta yi Allah wadai da jam'iyyar NNPP da shugabanninta bisa yin ƙage kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ƙungiyar na yin martani ne kan zargin da shugaban jam'iyyar na jihar Kano ya yi na cewa shugaba Tinubu na da hannu a rikicin masarautar Kano.
Kungiya ta tabo jam'iyyar NNPP
Martanin ƙungiyar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Alhaji Musa Mohammed, ya rabawa manema labarai a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙungiyar ya nuna kaɗuwarsa kan yadda shugaban na NNPP, Hashim Dungurawa ya yi kalamai domin ɓata sunan Shugaba Tinubu, rahoton jaridar Blueprint ya tabbatar.
Wane zargi aka yiwa Kwankwaso da NNPP?
ProFN ta zargi NNPP da ƙoƙarin kawo hargitsi na ƙabilanci da yaɗa ƙarairayi sannan ta buƙaci ta gaggauta janye munanan kalaman tare da ba ƴan Najeriya da Shugaba Tinubu haƙuri.
Ƙungiyar ta gargadi jam’iyyar da ta daina ɗora alhaki kan wasu na rashin taɓuka komai a zaɓen da ya gabata da rashin yin abin a zo a gani a jihar Kano.
"Mun ga ya dace mu shiga tsakani yanzu da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso suka ƙara faɗaɗa faɗan da suke yi zuwa kan shugaban ƙasan Najeriya, inda suke gaya masa maganganu saboda ya kare kundin tsarin mulkin Najeriya."
"Wannan abin kunya ne ga ƴan barandan NNPP. Dungurawa ya fara amfani da zaben 2027 yana barazana ga Shugaba Tinubu, wanda hakan ke nuna gwamnatin Kano ba ta san inda ta dosa ba."
- Alhaji Musa Mohammed
NNPP ta gargaɗi Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya yi tsokaci kan rigimar sarautar jihar.
Hashim Dungurawa ya ce rashin tsoma bakin Bola Tinubu a rigimar zai iya kawo masa cikas a zaben 2027 da ake fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng