CBN Ya Yi Albishirin Rage Kudin Ruwa, Watakila a Samu Sauki Bayan Korafin Dangote
- Babban bankin Najeriya (CBN) ya yiwa yan kasa albishir kan sassauta kuɗin ruwa ga masu karɓar bashi domin samar da saukin rayuwa
- Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ne ya bayyana haka yayin wani taron ƙaddamar da littafi a ranar Asabar da ta wuce a jihar Legas
- Hakan ya biyo bayan korafi da aka rika samun kan karin kudin ruwa ne daga yan kasuwa a Najeriya ciki har da Alhaji Aliko Dangote
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lagos - Babban bankin Najeriya ya bayyana aniyarsa ta rage kudin ruwa ga masu karbar bashi.
Hakan na zuwa ne bayan Alhaji Aliko Dangote ya yi korafi kan yadda yawan kuɗin ruwa zai durkusa sana'o'i a Najeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar Asabar ne mataimakin gwamnan CBN, Philip Ikeazor ya bayyana haka yayin da ya wakilci gwamnan bankin a wani taro a Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe CBN zai rage kudin ruwa?
A yayin taron, Philip Ikeazor ya bayyana cewa akwai ƙoƙari da CBN yake wajen ganin an samu ragi a kudin ruwa.
Mataimakin gwamnan CBN ya ce a nan gaba kadan bankin zai rage kudin ruwa domin daidaita lamura a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa wasu ƙasashen Turai ma sun yi karin kudin ruwa amma sun rage kudin bayan lamura sun daidaita, rahoton The Guardian.
CBN: 'Muna jin tsoron tashin farashi'
Babban bankin ya bayyana cewa suna daukan wasu matakai ne domin kaucewa mummunan tashin farashin kayyakki a Najeriya.
Philip Ikeazor ya ce akwai ƙasashe da suka samu kansu a cikin mummunan tashin farashi wanda har yanzu sun gagara fita.
A cewarsa, a dalilin haka ne bankin ya dauki wasu matakai ciki har da karin kudin ruwa domin ganin lamura sun daidaita a Najeriya.
CBN: 'Ku karbi lalatattun takardun Naira'
A wani rahoton, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ya samu korafe-korafe masu yawa kan bankuna ba sa karbar lalatattun takardun Naira.
Bankin CBN ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya takunkumi mai tsauri kan bankunan da aka kama suna kin karbar kudin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng