Jerin Gwamnnoni 10 da Suka Ba da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci a Jihohinsu

Jerin Gwamnnoni 10 da Suka Ba da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci a Jihohinsu

Akalla jihohi 10 a Najeriya sun ayyana ranar Litinin 8 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan Hijrah.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ana amfani da kwanan watan Hijirah ne domin tunawa da hijirar Manzon Allah (SallalLahu Alaihi Wasallam) daga Makka zuwa Madina a shekara ta 622 Miladiyya.

Kalandar Hijira ta ginu ne a kan zagayowar wata, kuma kowane wata yana farawa ne daga ranar da aka shaida ganin jinjirin sabon wata, kamar yadda shafin Islamic Relief ya nuna.

Gwamnonin Najeriya sun ayyana Litinin matsayin ranar hutun shigowar sabuwar shekarar Musulunci
Gwamnonin da suka ayyana hutun shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446AH. Hoto: @AAdeleke_01, @RealAARahman
Asali: Twitter

Sabuwar shekarar Musulunci, 1446AH

Sabuwar shekarar Musulunci a bana ta fara ne fara ne a ranar Lahadi 7 ga watan Yuli, wadda ta yi dai dai da ranar 1 ga watan Muharram, 1446 bayan Hijirah.

Kara karanta wannan

1446: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata Musulmi Ya Sani Dangane da Shekarar Hijira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin da suka ayyana Litinin matsayin ranar hutun zuwan sabuwar shekarar sun yi hakan ne saboda dama can ranar Lahadi ranar hutu ce a kasar.

Ga jerin jahohin da ma’aikata ba za su yi aiki a yau Litinin ba, saboda hutun sabuwar shekarar Musulunci ta 1446AH, kammar yadda jaridar Punch ta ruwaito:

1. Jihar Osun ta ayyana hutu

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin murnar zuwan sabuwar shekarar Musulunci.

A wata sanarwa da ta fito daga ofishin gwamnan, Adeleke ya taya al’ummar Musulmin jihar Osun murna, inda ya bukaci su yi amfani da wannan dama wajen yiwa jihar addu'o'i.

Ana dai kallon ayyana ranar hutun da gwamnan ya yi a matsayin nuna kaunarsa ga al’ummar Musulmin jihar wanda zai samu karbuwa.

2. Jihar Oyo ta ba da hutun kwana 1

Kara karanta wannan

1446AH: Gwamna Dikko Radda ya ayyana ranar hutu saboda sabuwar shekarar musulunci

Kamar takwaransa na jihar Osun, Gwamna Seyi Makinde na Oyo shi ma ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar da babu aiki domin murnar zuwan sabuwar shekarar Musulunci.

Gwamna Makinde, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bukaci al’ummar Musulmin Jihar Oyo da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa jihar addu’ar zaman lafiya, da hadin kai.

3. Gwamnan Jihar Kebbi ya ba da hutu

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris shi ma ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin zuwan watan Muharram. Hakan zai ba Musulmi damar murnar zuwan sabuwar shekara.

Gwamna Nasir Idris, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi kira ga daukacin mazauna jihar da su ci gaba da zama cikin aminci da mutunta addini da al’adun juna.

4. Kwara ta ba da hutun sabuwar shekara

Kwara ta bi sahun sauran jihohin da suka ayyana ranar hutu domin murnar zuwan sabuwar shekarar Musulunci, kamar yadda gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Malamai da limamai a Arewa sun yiwa masu son warware rawanin Sarkin Musulmi wankin babban bargo

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya sanar da ranar Litinin a matsayin ranar hutu a jihar Kwara, inda ya nemi al'ummar Musulmi su sanya jihar a cikin addu'o'insu.

5. Hijrah: Jigawa ta shiga jerin masu hutu

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan Hijirah.

Gwamnan ya sanar da hutun ne a wata sanarwa da ya fitar. Ya taya al’ummar Musulmin Jihar Jigawa murnar zagayowar wannan rana.

6. Kano ta ayyana hutun sabuwar shekara

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu tare da shiga cikin jerin sauran wadanda suka ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci.

Gwamna Abba ya ja kunnen ‘yan jihar da su yi amfani da hutun a matsayin lokacin da za su shirya yin ayyukan alkairi a cikin sabuwar shekarar.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi addu’ar Allah ya kara zaman lafiya da ci gaba a jihar da ma kasa baki daya.

Kara karanta wannan

1446AH: Gwamnatin Borno ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci

7. Mala Buni ya ba ma'aikata hutu

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1446AH.

Gwamna Buni, a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar Hamidu Alhaji ya fitar, ya bukaci ma’aikatan da su yi amfani da wannan lokacin wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya.

8. Bala Muhammad ya ayyana ranar hutu

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya ayyana ranar 2 ga Al-Muharram a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jihar domin girmama shigowar sabuwar shekarar Musulunci.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmin jihar da su rika gudanar da ayyukan da suke tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da fahimtar juna a wannan sabuwar shekarar ta 1446.

9. An ba da hutun kwana 1 a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar Litinin 8 ga watan Yuli, 2024 a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Kara karanta wannan

Sabuwar shekarar 1446AH: Gwamnatin Kano ta ayyana ranar hutu

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Yar’adua ya ce gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ne ya ayyana ranar hutun.

10. Borno ta ba da hutun sabuwar shekara

Gwamnatin jihar Borno ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2024, a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci.

Muƙaddashin gwamnan jihar, Umar Kadafur, a wata sanarwa a ranar Asabar ya bayyana cewa ranar Litinin ta zama ranar hutu a faɗin jihar.

Abubuwan sani game da shekarar Hijirah

A jiya Lahadi ne aka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1446. Hakan na nuni da cewa Hijirar da Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi daga Makka zuwa Madina ta cika shekaru 1446.

Legit ta yi bincike kan abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ku sani a kan tarihin Hijirah da sauransu, wanda za ku karanta a nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.