An Shiga Jimamin Bacewar Yarinya Bayan Kwale Kwale Ya Kife da Yan Kasuwa a Jigawa

An Shiga Jimamin Bacewar Yarinya Bayan Kwale Kwale Ya Kife da Yan Kasuwa a Jigawa

  • Rahotanni na nuni da cewa an samu kifewar kwale kwale da wasu yan kasuwa a jihar Jigawa da ke Arewa maso yammacin Najeriya
  • Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin ta kuma yi bayani kan irin asarar da aka tafka yayin hadarin
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu Adam ne ya bayyana hakikanin abin da ya faru da kuma yin kira ga al'umma kan yaɗa jita jita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - A daren jiya Lahadi aka samu kifewar kwale kwale a karamar hukumar Auyo ta jihar Jigawa.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar haɗarin inda ta bayyana adadin mutanen da suka rasu.

Kara karanta wannan

Matashi ya sassara tsohuwa mai shekaru 60 da makami, ya kasheta har lahira

Kwale kwale ya kife
Kwale kwale ya kife da yan kasuwa a Jigawa. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sako da kakakin rundunar yan sanda a jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kifewar kwale kwale: An samu mutuwa

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa kifewar kwale kwalen ya jawo hasarar ran wata mata daya.

Yan sanda sun bayyana cewa akwai wata wata mata da ake nema tun jiya amma har yanzu ba a samu gano ta a cikin ruwan ba.

Hadarin ya ritsa da yan kasuwa 20 ne cikin dare inda aka ceto 18 da ransu, daya ta mutu sannan ana neman daya har yanzu.

Rahotannin da suka fito daga baya sun nuna cewa an samu matar data bace amma babu rai wanda hakan ke nuni da cewa mata biyu ne suka rasu.

Kara karanta wannan

An kama mahaifin da ya daure dansa bayan sun rabu da mahaifiyar yaron

Dalili kifewar kwale kwale a Jigawa

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa kwale kwalen ya kife ne sakamakon iska mai karfi da aka samu, rahoton Channels Television.

An samu iska kuma matukin ya ɗibi mutane da suka wuce ƙima a dalilin haka ne ya gagara shawo kan kwale kwalen har ya kai ga kifewa.

Har ila yau, kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu Adam ya gargadi al'umma kan yaɗa labaran da ba su da asali musamman a lokutan haɗura.

Kwale kwale ya kife a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane masu tserewa hare-haren ƴan bindiga sun rasa rayukansu bayan kwale-kwalensu ya kife a tsakiyar Kogi a jihar Neja.

Mutum huɗu ne suka rasa rayukansu waɗanda suka fito daga ƙauyen Gurmana a ƙaramar hukumar Shiroro sakamakon aukuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng