Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum 10 a Kebbi
- Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyar rasa rayuka 10 a karamar hukumar Jega da ke jihar Kebbi
- An tattaro cewa mamatan wadanda suka kasance mata na a hanyarsu ya zuwa bikin aure ne daga Madauci zuwa kauyen Tungan Gehuru
- Shugaban karamar hukumar, Barista Shehu Marshal; ya tabbatar da faruwar lamarin cewa tuni aka samo gawarwakin mutum hudu
Mutane goma sun mutu a wani kifewar kwale-kwale da ya afku a ranar Litinin, a karamar hukumar Jega da ke jihar Kebbi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Bincike sun nuna cewa mamatan wadanda suka kasance mata na a hanyarsu ya zuwa bikin aure ne daga Madauci zuwa kauyen Tungan Gehuru.
Kwale-kwalen ya kife ne da misalin karfe 4:00 na rana a ranar Litinin yayinda yake dauke da fasinjoji 10.
Da yake hira da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, shugaban karamar hukumar, Barista Shehu Marshal; ya tabbatar da faruwar lamarin cewa tuni aka samo gawarwakin mutum hudu.
KU KARANTA KUMA: Miji ya kashe matarsa da yaransa biyu saboda sun dame shi da surutu
“An samo gawarwakin mutum hudu kuma tuni aka binne su. Tawagar ceto na aiki domin nemo sauran mutane shida” in ji Marshal.
A wani labari makamancin haka, mun ji a baya cewa wasu mutum uku da aka bayyana a matsayin Melody M, Isaac G., da James S., sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a jihar Adamawa.
Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa mutanen, wadanda suka kasance maza biyu da mace guda, sun nitse ne a yayinda suke a hanyarsu ta zuwa bikin binne wani a karamar hukumar Lamurde bayan kwale-kwalen ya kife.
Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban karamar hukumar Lamurde, Burto Williams, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.
“Hatsarin abun bakin ciki ne da yake bukatar gwamnati ta kawo agaji ga mutanen yankin wadanda ruwa ke yawan yi wa barna.
“Karamar hukumar Lamurde na kokarin samar da kulawar likitoci ga wadanda suka tsira yayinda hukumar za ta dauki nauyin birne mutum uku da suka mutu,” in ji Burto.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng