1446: Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Musulmi Ya Sani Dangane da Shekarar Hijira
- A jiya Lahadi ne aka shiga 1 ga watan Muharram wanda hakan ya yi nuni da cewa an shiga sabuwar shekarar Musulunci
- A bisa lissafi, an shiga shekara ta 1446 tun bayan Hijirar Annabi mai tsira da aminci daga garin Makka zuwa birnin Madina
- A wannan rahoton, Legit tattaro muku abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ku sani a kan amfani da lissafin Hijira a Musulunci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A jiya Lahadi al'ummar Musulmi a Najeriya da fadin duniya suka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1446.
Hakan na nuni da cewa Hijirar da Annabi Muhammad (Tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya yi daga Makka zuwa Madina ta cika shekaru 1446.
Legit ta yi bincike kan abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ku sani a kan tarihin hijira da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe aka fara lissafin Hijira?
An fara lissafi da kalandar Hijira ne a lokacin mulkin Umar Ɗan Khaɗɗabi kamar yadda Sheikh Muhammad Salih ya bayyana a shafinsa.
Tun daga lokacin al'ummar Musulmi suka fara lissafin kwanan wata da kalandar Musulunci har zuwa yau.
Dalilin fara kalandar shekarar Hijira
An ruwaito cewa an samu saɓani tsakanin mutane biyu a kan bashi, ana maganar za a biya kuɗin a watan Sha'aban amma an gagara gane shekarar.
Bayan maganar ta kai gaban Umaru Ɗan Khaɗɗabi sai ya tara mutane domin shawara kan sanya kalandar da za su rika amfani domin rarrabe tsakanin shekaru.
Bayan tattaunawa a yayin taron ne aka cimma matsaya kan fara amfani da kalandar Musulunci ta Hijira.
Meyasa aka zabi shekarar Hijira?
Umaru Ɗan Khaɗɗabi ya zabi Hijira ta kasance farkon lissafin kalandar Musulunci ne saboda Hijira ta shahara a tsakanin al'umma baki daya kuma babu saɓani a kan ranar da aka yi ta.
Sheikh Abdulaziz AT-Tarefi ya bayyana a shafinsa na Telegram cewa an zaɓi hijira ne domin nuna addinin Musulunci ya bayar da fifiko a kan ayyuka maimakon ranakun bukukuwa.
Watanni nawa ake da su shekarar hijira?
Shekarar hijira ta na da watanni guda 12 kamar yadda kalandar bature ke da su. Ga watannin kamar haka:
- Muharram
- Safar
- Rabi'ul Awwal
- Rabi'ul Sani
- Jumada Ula
- Jumada Akhir
- Rajab
- Sha'aban
- Ramadan
- Shawwal
- Zul Qadah
- Zul Hijjah
Hijira: An ba da hutu a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ba da hutun domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH.
Gwamnatin ta ayyana yau Litinin, 8 ga watan Yulin 2024 a matsayin ranar da ma'aikata ba za su je wuraren aiki ba a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng