Saudi ta koma amfani da kalandar shekarar Bature

Saudi ta koma amfani da kalandar shekarar Bature

- Yayin da aka shiga sabuwar shekarar musulunci, Kasar Saudi ta koma amfani da shekarar Bature

- Sarki Salman ya koma amfani da Kalandar shekarar bature ne domin tsuke bakin aljihun Gwamnati

- Kasar Saudi na fama da matsalar tattali tun bayan faduwar farashin mai a duniya

Saudi ta koma amfani da kalandar shekarar Bature
Saudi Arabia na fama da matsalar rashin kudi

 

 

 

 

 

 

Yayin da aka shiga sabuwar shekarar Hijrah na musuluci, Kasar Saudi ta daina amfani da shekarar Hijrah, ta koma na bature. Saudi ta dauki matakin komawa amfani da kwanakin watan bature domin biyan ma’aikata albashi da kuma aikin makaranta. Kasar dai tayi haka ne domin tsuke bakin aljihun Gwmanati.

Sarki Salman na Kasar Saudi ya dauki matakin amfani da kalandar bature ta Girigori wajen kidayar kwanakin shekara a Kasar. Saudi dai ta shiga wani hali ne tun bayan karyewar darajar man da ta dogara da shi a duniya. Ministocin Kasar Saudi sun amince da wannan sauyin lamba tun a wancan makon.

KU KARANTA: Murnar Yancin Kai; Yar Nollywood tayi tsirara

Kasar dai ta dauki wannan mataki ne domin halin da ta fada na tattalin arziki. BBC ta rahoto cewa Kasar ta kara kudin takardun shigan ta, tana kuma rage wasu alawus na ma’aikata, kuma za ta rage albashin ‘yan Kasar da Ministoci. A baya dai Saudi ta salami na’iban limaman Kasar har 10000 saboda rashin kudi. Saudi dai ta fi kowa fitar da man fetur, sai dai ta gamu da kalubale bayan karyewar farashin mai a duniya

Akwai dai bambanci tsakanin shekarar Hijra ta Annabi Muhammadu da kuma kalandar miladiyya ta haihuwar Annabi Isa da kwanaki kusan goma sha daya. Saboda kwanakin watannin Hijira ba su wuce 29 ko 31, inda da bature kuma yana kai har 31. Tun a Tarihi dai Saudi ba ta taba amfani da kalandar Bature ba sai wannan karo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng