'Yan Bindiga Sun Yiwa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna, Sun Hallaka Mutum 4

'Yan Bindiga Sun Yiwa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna, Sun Hallaka Mutum 4

  • Ƴan bindiga sun yiwa jami'an tsaro na ƴan banga kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Njaba ta jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabas
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka ƴan banga uku tare da wani yaro yayin harin wanda suka kai a yammacin ranar Lahadi
  • Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce ta tura tawaga ta musamman domin cafko maharan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Wasu ƴan bindiga sun kashe ƴan banga uku da wani yaro yayin wani hari da suka kai a jihar Imo.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a Umuaka, da ke ƙaramar hukumar Njaba ta jihar Imo a yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi dare sun sace 'yan jarida 2 tare da iyalansu a Arewa

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Imo
'Yan bindiga sun hallaka 'yan banga a jihar Imo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan banga

Wata majiya ta ce ƴan bangan na sintiri ne a cikin wata mota a lokacin da ƴan bindigan suka kai musu farmaki a Afor Umuaka, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyar, maharan sun yi kwanton ɓauna ne inda suka buɗe wuta kan jami'an tsaron.

Wani harsashi ya samu yaron inda ya ce ga garinku nan a wurin da lamarin ya auku, rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an tura tawaga ta musamman domin cafko maharan.

"Kwamishinan ƴan sandan jihar Imo, CP CP Aboki Danjuma, ya yi Allah wadai da kisan da ƴan bindiga suka yiwa ƴan banga a ƙauyen Umuaka a ranar Lahadi, 7 ga watan Yulin 2024."

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan tsige 'yan majalisa 25 da suka sauya bar PDP zuwa APC

"Bisa wannan mummunan lamarin da ya jawo asarar rayukan ƴan banga da wani mutum ɗaya, kwamishinan ya tura tawaga ta musamman da kayan aiki tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin farauto maharan da suka kai harin."

- Henry Okoye

Karanta wasu ƙarin labaran ƴan bindiga

Ƴan sanda sun cafke shugaban ƴan banga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sanda a jihar Rivers ta kama wani shugaban yan banga ɗauke da sassan jikin ɗan Adam a ƙaramar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni.

Biyo bayan kama shugaban mai suna Felix Nwaobakata, rundunar ta ƙara kai samame kan wasu ƴan banga a yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng