1446AH: Gwamna Dikko Radda Ya Ayyana Ranar Hutu Saboda Sabuwar Shekarar Musulunci
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ba da hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH
- Gwamnan ya ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar da babu aiki saboda sabuwar shekarar da ta fara a ranar Lahadi
- Radda ya buƙaci malamai da su ci gaba da yin nasiha kan zaman lafiya tare da addu'ar Allah ya kawo ɗauki kan matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2024 a matsayin ranar hutu a jihar.
Gwamna Radda ya ba da hutun ne domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH.
1446AH: Gwamnatin Katsina ta ba da hutu
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari, ya sanyawa hannu, wacce hadimin gwamnan Isah Miqdad ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mai girma gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ayyana ranar Litinin 8 ga Yuli, 2024 daidai da 2 ga watan Al-Muharram, 1446AH a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci."
"Gwamna Dikko Radda ya ce an ayyana ranar Litinin a matsayin ranar da babu aiki domin ba dukkanin ma’aikatan jihar damar haɗa kai da sauran al’ummar Musulmi domin murnar shiga sabuwar shekara ta 1446AH."
- Abdullahi Garba Faskari
Gwamna Radda ya musulmai murnar sabuwar shekara
Gwamna Dikko Radda ya taya ɗaukacin al’ummar musulmin jihar da ma duniya baki ɗaya murnar shiga sabuwar shekara da ta fara a ranar Lahadi, 1 ga watan Al-Muharram 1446AH wanda yake daidai da 7 ga watan Yulin 2024.
Gwamnan ya yi kira ga malamai da su ci gaba da yin nasiha kan zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar da addu’ar Allah maɗaukakin Sarki ya kawo ɗauki kan matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Gwamna Radda ya buƙaci addu'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya buƙaci al'ummar jihar da su yi addu'o'i domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
Gwamna Dikko Radda ya buƙaci al'ummar musulmin su roƙi Allah maɗaukakin Sarki ya kawo ƙarshen matsalar wacce ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng