Sanusi vs Aminu Ado: An Fadi Matsalar da Tinubu Zai Samu a Kano a Siyasa
- Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, ya gargaɗi shugaban ƙasa Bola Tinubu kan shiga cikin rikicin masarautar Kano
- Hashim Dungurawa ya bayyana cewa shugaban ƙasan zai samu matsala a jihar Kano a zaɓen 2027 saboda katsalandan a rikicin masarautar Kano
- Ya kuma zargi shugaban ƙasan da goyon bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, saboda yana da tsatson Yarabawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, Hashim Dungurawa, ya yi zargin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu na ƙoƙarin kawo hargitsi a jihar.
Hashim ya yi zargin cewa shugaban ƙasan yana son ɗora Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, kan sarautar Kano saboda su duka biyun suna da tsatson Yarabawa.
Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano kan nasarorin da jam’iyyar NNPP ta samu a jihar cikin shekara ɗaya, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin sarauta: Wane zargi aka yi kan Tinubu?
Hashim Dungurawa ya bayyana cewa babu dalilin da zai sanya sojojin Najeriya, ƴan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro za su ba Sarki Aminu Ado Bayero kariya ta musamman duk da gwamnatin jihar ba ta so.
Ya yi gargaɗin cewa kutsen da ake zargin Shugaba Tinubu ya yi a rikicin masarautar Kano zai jawo masa matsala a zaɓen 2027, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
"Matsayarka kan rikicin masarautar Kano tabbas za ta ba ka matsala a 2027, saboda idan kana tunanin za ka yi amfani da hakan domin samun Kano, idan lokaci ya yi za ka gane kuskurenka."
"Idan shugaban ƙasa yana tunanin zai yi amfani da wasu na kusa da shi a Kano da tatson Bayero na Yarbawa domin ci gaba da barin Aminu Ado Bayero a Kano, ya jira 2027, za mu nuna masa cewa waɗannan mutanen ba za su taimaka masa ba."
- Hashim Dungurawa
Daga nan sai ya buƙaci shugaban ƙasan da ya yi duk abin da zai iya domin kawo ƙarshen rikicin masarautar Kano ta hanyar tabbatar da cewa an raba Sarkin Kano na 15 da jihar.
Karanta wasu labaran kan rikicin sarautar Kano
- Sanusi II vs Aminu: Sheikh Dutsen Tanshi ya dauki zafi kan rigimar Kano, ya fadi matsayarsa
- "Da kun yi koyi da magabatanku": Farfesa ya shawarci Aminu Ado da Sanusi II
- Sarautar Kano: Lauyoyi sun bayyana dalilin janye jiki su bar shari'ar Aminu Ado a kotu
Laƙanin kayar da Tinubu a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon jigo a jam'iyyar APC, Salihu Lukman ya yi kira ga manyan ƴan siyasa a Najeriya da su dunƙule waje ɗaya domin kawar da APC daga kan madafun iko.
Salihu Lukman wanda ya yi murabus daga APC ya yi kira ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso da Rotimi Amaechi da su haɗa kai domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng