1446AH: Gwamnatin Borno Ta Ba da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci
- Gwamnatin jihar Borno ta ba da hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH
- Muƙaddashin gwamnan jihar Umar Kadafur ya ce gwamnatin ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar
- Ya buƙaci al'ummar musulmai da su zauna lafiya da mabiya sauran addinai tare da yin riƙo da halaye masu kyau da nagarta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2024, a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci.
Muƙaddashin gwamnan jihar, Umar Kadafur, a wata sanarwa a ranar Asabar ya bayyana cewa ranar Litinin ta zama ranar hutu a faɗin jihar.
Umar Kadafur ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin girmama sabuwar shekarar Musulunci wacce za ta fara a ranar Lahadi, 1 ga watan Muharram 1446AH, cewar rahoton jaridar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Borno ta ba da hutu
A cewarsa, hutun na da nufin ba al’ummar musulmi damar yin tunani a kan muhimmancin Hijira da kuma gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci cikin haɗin kai da sadaukarwa.
The Punch ta ce muƙaddashin gwamnan ya miƙa saƙon fatan alheri ga al’ummar musulmin Borno da ma na duniya baki ɗaya, tare da bayyana fatan samun sabuwar shekarar Musulunci mai cike da zaman lafiya, lumana da albarka.
Ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su yi riƙo da ɗabi’u na ƙanƙantar da kai, juriya, mutuntawa, mutunci da kishin ƙasa, waɗanda suka dace da duniya baki ɗaya.
Umar Kadafur ya kuma ja hankalin al’ummar musulmi da su zauna lafiya da mabiya sauran addinai, tare da ƙarfafa ƴan uwantaka domin samun haɗin kai.
Gwamnatin Kano ta ba da hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar.
Gwamnatin ta ba da hutu a ranar ne domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH.
Asali: Legit.ng