Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar musulunci

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar musulunci

- Gwamna Abdullahu Umar Ganduje na Kano bada hutun aiki a ranar Alhamis a jihar domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci

- Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da Hadimin gwamnan da shafin gwamnatin jihar suka wallafa a twitter

- Ganduje ya yi kira ga al’ummar Musulmin jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya da karuwar arziki

Gwamnatin jihar Kano ta bada hutun aiki a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci.

Sanarwar hakan ta fito ne cikin wani sako da hadimin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan sabuwar hanyar sadarwa ta zamani, Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Musulmin jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya da karuwar arziki.

Ganduje ya kuma yi addu’a kan Allah ya kawo wa jihar dauki daga annobar korona da kuma matsin da mutane suke ciki.

Gwamnatin kano ta bada hutun sabuwar shekarar musulunci
Gwamnatin kano ta bada hutun sabuwar shekarar musulunci Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Har ila yau sanarwar ta kuma yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah a cikin dukkannin al’amuransu tare da zama masu yafiya kamar yadda Musulunci ya tanadar.

Ganduje ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa rayuwar al’ummar jihar, kamar yadda shafin gwamnatin Kano ta twitter ta wallafa.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: An garkame mai kamfanin gidajen mai na Rahamaniyya a kasar Burtaniya

A gobe Alhamis, za ta kasance 1 ga watan farko a Kalandar Musulunci wato Al- Muharram, shekara 1442 bayan hijira daga Birnin Makka zuwa Madinah ta Fiyayyen Hallita, Annabi Muhammad, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Ganduje ya faɗa wa shugaban hukumar sauraron ƙorafin jama'a da yaƙi da rashawa ta jihar, Muhyi Rimingado ya yi aikinsa ba tare da sani ko sabo ba.

Ganduje ya kuma fada wa Ramingado kada ya ɗaga wa kowa ƙafa wurin yaƙi da rashawa ko da ƴan fadar gwamna ne.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyara hedkwatar hukumar a ranar Asabar domin duba aikin gyara da kwaskwarima da ake yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng