Gwamnati Ta Ba Masu Sana’ar PoS Sabon Umarni Yayin da Wa’adin Rijista da CAC Ya Kare

Gwamnati Ta Ba Masu Sana’ar PoS Sabon Umarni Yayin da Wa’adin Rijista da CAC Ya Kare

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da tsawaita wa'adin watanni biyu da ta baiwa masu sana'ar PoS domin su yi rijista da hukumar CAC
  • Hukumar ta CAC ce ta fitar da wannan sanarwar a rana Asabar inda ta ce an tsawaita wa'adin da kwana 60, zuwa 5 ga watan Satumba
  • A cewar CAC, wannan karin zai baiwa masu sana'ar PoS da ke karkara, wadanda ke fuskantar matsalar sadarwa damar yin rijista

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Bayan karewar wa'adin watanni biyu da aka dibar masu, hukumar kula da kamfanoni (CAC) ta tsawaita wa’adin rajistar sana'a ga masu PoS zuwa ranar 5 ga Satumba.

Hukumar ta ce an tsawaita wa’adin farko na ranar 7 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Satumba; karin kwanaki 60 domin ba masu sana'ar PoS damar yin rijista.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar Rarara ta rasa ranta a hannun ƴan bindiga? Gaskiya ta bayyana

Gwamnati ta yi magana kan rijistar masu sana'ar PoS
Hukumar CAC ta tsawaita wa'adin rijistar sana'a ga masu PoS zuwa 7 ga watan Yuli. Hoto: Getty Images.
Asali: UGC

Hukumar ta CAC ta sanar da tsawaita wa’adin ne a ranar Asabar a cikin wata sanarwa da fitar kuma aka rabawa manema labarai, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CAC ta tsawaita rijistar masu PoS

Hukumar ta ce matakin tsawaita wa'adin na da nufin samar da isasshen lokaci ga masu gudanar da sana'ar PoS su kammala rajistar sana'arsu.

Jaridar Tribune ta ruwaito sanarwar ta ce:

“Hukumar kula da kamfanoni tana son sanar da masu sana'ar PoS cewa an tsawaita wa’adin farko na 7 ga Yuli 2024 na rijistar sana'o'in su zuwa ranar 5 ga Satumbar 2024.
"Wannan zai baiwa masu sana'ar da ke karkara, waɗanda wataƙila suke fuskanci ƙalubalen sadarwa wajen yin rajistar damar kammala rijistar cikin sauki."

CAC ta umarci masu PoS su yi rijista

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnati ta ba kamfanonin kamfanonin da ke sarrafa na'urar PoS wa'adin watanni biyu su yi wa abokan huldarsu rijista da hukumar CAC.

Shugaban hukumar kula da kamfanoni (CAC), Hussaini Ishaq Magaji ya ce yi wa masu sana'ar PoS rijista zai kare kasuwancinsu daga 'yan zamba da kuma kutse.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.