An Tashi da Jimami a Arewa, ’Yan Bindiga Sun Yi Asubanci, Sun Sace Mata Mai Ciki, Wasu 4

An Tashi da Jimami a Arewa, ’Yan Bindiga Sun Yi Asubanci, Sun Sace Mata Mai Ciki, Wasu 4

  • An shiga tashin hankali a Niger yayin da ‘yan bindiga suka farmaki wani gida tare da sace mutane sama da 4 cikin dare
  • Rahoto ya bayyana yadda ‘yan ta’addan suka yi saraf tare da shiga gida, inda suka sace mace mai juna biyu tare da danta
  • Watanni sama da hudu kenan ‘yan yankin ke zaune ba tare da fuskantar harin ‘yan ta’adda ba, sun tashi da jimami a makon nan

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Niger - Sararawar watanni hudu da al’ummar Garam a jihar Niger suka samu ya samu tasgaro a safiyar Asabar lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a unguwar, suka yi garkuwa da wata mata mai juna biyu da kuma wasu mutane hudu.

Kara karanta wannan

Wuce gona da irin Isra'ila: Isra'ila ta farmaki makarantar majalisar dinkin duniya a Gaza

Garam, unguwar da ke kan iyaka da Karamar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya (FCT), ta shiga cikin rudani tsakanin watan Disamban 2023 da Fabrairun 2024 lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hare-hare fiye da sau hudu, inda aka yi garkuwa da mutane da dama.

'Yan bindiga sun sace mutane a Niger
An sace mata mai ciki da mijinta a Niger
Asali: Original

Duk da cewa al'ummar sun dan ji dadin hutun da suka samu, ‘yan bindiga sun sake kai farmaki tare da tafka mummunan barna, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna sun fadi bala’in da suka ji

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun shigo unguwar ne ta daji da misalin karfe 3 na asuba a ranar Asabar, kuma suka shiga gidan wadanda suka yi garkuwa da su.

Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigar ba su harba bindiga sama ba don kaucewa ankarewar jami’an tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan bindiga sun turo saƙon bidiyon mutanen da suka sace a Maidabino

A cewar majiyar:

“Mun ji cewa sun zo da misalin karfe 3:00 na asuba. Sun yi garkuwa da mutane biyar ciki har da wata mata mai juna biyu tare da yaronta da mijinta.”

Yadda ‘yan bindigan suka kutsa gidan mutane

Majiyar ta kuma bayyana yadda ‘yan ta’addan suka shiga gida, inda tace:

“Sun kutsa cikin gidan ne ta hanyar tura kofa da karfi. Sun zo cikin sirri ba tare da harba bindiga ba kamar yadda suke yi a baya.
“Matar mai juna biyu da mijinta ‘yan kabilar Nupe ne tare da dansu, sun kuma yi garkuwa da wani Bahaushe da kwanan nan ya shigo gidan da kuma wani yaro.”

An sace alkaliya da ‘ya’yanta a Kaduna

A bangare guda, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata alkaliyar kotu, Janet Galadima-Gimba, tare da ‘ya’yanta maza hudu a Kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun sace alkaliyar da ‘ya’yanta a gidansu da ke unguwar Mahuta a Kaduna a ranar 23 ga watan Yuni.

‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da su, wadanda adadinsu ya kai 15, sun kai farmaki gidan ne da daddare a lokacin da mijinta wanda likita ne, yake wajen aiki, cewar rahoton jaridar TheCable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.