Samoa: Tinubu Zai Dauki Mataki Kan Daily Trust Game da Rahoton Yarjejeniyar da Aka Yi
- Yayin da rahoton yarjejeniyar Samoa ya bayyana, Gwamanti Tarayya ta shirya daukar mataki kan jaridar Daily Trust
- Jaridar ce ta fara buga rahoton wanda ake zargin akwai halasta auren jinsi a cikin tsare-tsaren yarjejeniyar
- Sai dai gwamnatin ya ƙaryata sanya hannu domin auren jinsi inda ta ce ta yi ne domin bunkasa tattalin arziki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya daukar matakin kotu kan jaridar Daily Trust game da rahoton Samoa.
Gwamnatin ta ce rahoton an buga ne domin bats mata suna duba da yarjejejeniyar ba ta da alaka da abin da aka wallafa.
Samoa: Gwamnatin Tinubu ta fusata
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da hadimin Bola Tinubu, Daddy Olusegun ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka a yau Asabar 6 ga watan Yulin 2024 a Abuja.
Idris ya ce duk da Tinubu ya sakewa ƴan jaridu fuska wurin gudanar da ayyukansu amma sun fara wuce gona da iri.
Ya ce Daily Trust ta sha buga rahotannin karya ga Gwamanti Tarayya ana kawar da kai amma wannan ya wuce gona iri.
Samoa: Tinubu zai dauki matakin shari'a
"Mun kadu da irin rahotanni da ake bugawa wanda ke barazana ga tsaron kasa, a baya muna kawar da kai wurin ganin hakan ba matsala, amma yanzu abin ya fara wuce gona da iri."
"A ƴan watannin nan, Daily Trust tana buga rahotanni marasa tushe wadanda ke neman batawa gwamnati suna da ba za a iya barinsu ba."
"Tun bayan juyin mulkin Nijar jaridar ta ke buga rahotannin ingiza al'umma, ta kawo rahoton kafa sansanin sojojin Amurka a Najeriya da sauya sunan filin jirgin saman Murtala Mohammed zuwa Wole Soyinka wadanda ba gaskiya ba ne."
"A yanzu ta na neman ingiza mutane kan rahoton Samoa wanda ya jawo malaman Addini suke ta huduba kan lamarin."
- Mohammed Idris
Sheikh Jingir ya magantu kan yarjejeniyar Samoa
A wani Labarin, kun ji cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu.
Shehin malamin ya yi fatali da yarjejeniyar inda ya ce ko kusa ba za a amince da wannan iya shege ba a Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng