Katsina: 'Yan Bindiga Sun Turo Saƙon Bidiyon Mutanen da Suka Sace a Maidabino

Katsina: 'Yan Bindiga Sun Turo Saƙon Bidiyon Mutanen da Suka Sace a Maidabino

  • Yan bindiga sun turo sakon faifan bidiyo kan mutanen da suka yi garkuwa da su a garin Maidabino, ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina
  • A bidiyon, mutanen waɗanda mafi akasari mata ne da ƙananan yara sun roki gwamnati ta taimaka ta kubutar da su
  • Haka nan kuma ƴan bindigar sun yi barazanar cewa za su kai hari cikin garin Ɗanmusa a cikin makon nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙatsina - ‘Yan bindiga sun turo saƙon wani faifan bidiyo da ke nuna wadanda suka yi garkuwa da su a garin Maidabino da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

A ranar 22 ga watan Yuni, ‘yan fashin daji suka tarwatsa Maidabino, birni na uku mafi girma a Danmusa, inda suka kashe mutane kusan tara tare da yin garkuwa da wasu 50, galibi mata da yara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun saki alkalin kotun Kaduna, amma sun rike 'ya'yanta 4, suna neman N150m

Taswirar jihar Katsina.
Yan bijdigar da suka sace mutane a Maidabino sun turo sakon bidiyo
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka shiga Maidabino

Rahotan Daily Trust ya ce maharan sun shafe sa’o’i da dama suna aikata abin da suke so ba tare da an taka masu birki ba saboda yawansu kuma an ce harin na ɗaukar fansa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A harin, sama da gidaje 10, shaguna 15, da motoci akalla tara ne ‘yan ta’addan suka kona daga karfe 10 na daren ranar Asabar har zuwa karfe 2:30 na safiyar Lahadi.

Ƴan bindiga sun turo saƙon bidiyo

Kwanaki kaɗan bayan wannan mummunan lamarin, ‘yan fashin sun turo sakon wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna 5 da dakika 41, inda suka nuna mutanen da suka sace.

Mutanen da ƴan ta'addan suka sace sun roƙi gwamnati ta taimaka ta ceto su daga hannun ƴan bindigar.

A bidiyon, ƴan bindigar sun bayyana cewa dakarun rundunar ƴan sa'kai na Raɗɗa sun takura masu da kashe matansu da ƴaƴansu, hakan ya sa suka kai farmaki Maidabino.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutum 116 sun rasu a wurin taron addini

Sun yi barazanar shiga Ɗanmusa

Sun kuma bayyana cewa garin Ɗanmusa ne abin harinsu na gaba, inda suka fito fii suka sanar da cewa za su farmaki garin a cikin mako guda.

A bidiyon an ji ɗaya daga cikin ‘yan ta’addan sanye da kakin sojoji kuma riƙe da bindiga yana cewa ko gwamnan jihar ba zai iya kubutar da mutanen da ke hannunsu ba sai ta hanyar lalama.

"Kun gani ƴan sa'kai sun jawo maku kuma ba za su iya cetonku ba, ko Gwamna Radɗa ba zai iya cetonku ba indai ba ta hanyar lalama ba," in ji shi.

An kashe ƴan sanda 6 a Katsina

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun yiwa ayarin jami'an tsaro kwantan ɓauna a yankin ƙaramar hukumar Jibia da ke jihar Katsina da safiyar ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun kashe ƴan sanda huɗu nan take, sannan wani ɗaya ya rasu bayan an kai shi asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262