Sabuwar Shekarar 1446AH: Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutu

Sabuwar Shekarar 1446AH: Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutu

  • Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ba da hutun domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH
  • Gwamnatin ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yulin 2024 a matsayin ranar da ma'aikata ba za su je wuraren aiki ba a jihar
  • A cikin sanarwar wacce kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya fitar, gwamnatin ta buƙaci al'ummar jihar da su ci gaba da addu'o'in samun zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar.

Gwamnatin ta ba da hutu a ranar ne domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Uba Sani ya mayar da basaraken da El-Rufai ya tsige kan kujerarsa

Gwamnatin Kano ta ba da hutu
Gwamnatin Kano ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Shekarar 1446AH: Gwamnatin Kano ta ba da hutu

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Baba Dantiye ya fitar ranar Juma’a, 5 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci al'ummar jihar da su yi amfani da hutun wajen yin tunani a kan shekarar da ta gabata da kuma gudanar da ayyuka masu amfani, rahoton Within Nigeria ya tabbatar.

"Gwamna ya buƙaci al'ummar jihar da su yi amfani da hutun wajen yin tunani kan shekarar da ta wuce tare da yin abubuwa masu amfani waɗanda za su kawo sauƙi a wannan mawuyacin lokacin."
"Gwamnatin jiha a nata ɓangaren za ta ci gaba da aiwatarwa tare da ɓullo da tsare-tsare da za su ba ƴan jihar damar dogaro da kai."

Kara karanta wannan

1446AH: Gwamnati ta ba da hutu domin zuwan sabuwar shekarar musulunci

"Gwamna Abba ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a jihar da ma ƙasa baki ɗaya."

- Baba Dantiye

Ya kuma bayyana fatansa cewa samun addu’o’i da goyon bayan al’umma, zai sanya gwamnatinsa ta kai jihar zuwa tudun mun tsira tare da mayar da ita a matsayin zakaran gwajin dafi a ci gaban tattalin arziƙi tsakanin takwarorinta a ƙasar nan.

Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da yake yi na magance matsalolin ƴan fansho da maida hankali kan ilimin yara mata.

Sanusi II ya ƙara da cewa gwamnati mai ci a Kano ta mayar da hankali ga ƴan fansho da a baya aka jefa su cikin mawuyacin hali saboda rashin biyan su haƙƙoƙinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng