Tudun Biri: Gwamnatin Tinubu Ta Tuna da Mutanen da Sojoji Suka Jefa Wa Bam a Kaduna
- Sanata Kashim Shettima ya isa Kaduna domin ɗora harsashin fara aikin gina kauyen Tudun Biri a ƙaramar hukumar Igabi
- Hakan na ɗaya daga cikin alkawarin da gwamnatin tarayya ta ɗauka bayan kuskuren jefa bam kan masu taron Maulidi a watan Disamba
- Gwamna Malam Uba Sani da tawagar jami'an gwamnatin Kaduna ne suka tarbi Shettima a filin jirgin sama ranar Jumu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima ya ziyarci jihar Kaduna domin kaddamar da fara aikin sake gina ƙauyen Tudun Biri.
Idan zaku iya tunawa jirgin yaƙin rundunar sojojin Najeriya ya jefa bama-bamai kan masu taron Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna.
Lamarin wanda hukumar sojojin ƙasa ta ce kuskure ne ya auku ne ranar 3 ga watan Disamba, 2023 kuma ya laƙume rayukan mutane sama da 100 galibi ƙananan yara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kashim Shettima ya isa Kaduna
Channels tv ta ruwaito cewa mataimakin shugaban ƙasa ya isa jihar Kaduna domin kaddamar da fara aikin da aka yiwa mazauna garin alƙawari.
Gwamnan Kaduna Malam Uba Sani da wasu manyan jami'an gwamnatinsa ne suka tarbi Shettima a filinin jirgin sama ranar Jumu'a, 5 ga watan Yuli, 2024.
Sauran waɗanda suka je tarban mataimakin shugaban kasar sun haɗa da Darakta-Janar na hukumar da bada agajin gaggawa, kakakin majalisar dokokin Kaduna da sauransu.
Gwamnati za ta gina gidaje a Tudun Biri
Yayin ziyarar da zai kai Tudun Biri, mataimakin shugaban kasar zai kaddamar da harsashin ginin gidaje ga wadanda harin bam din soja ya rutsa da su a ranar 3 ga Disamba.
Sake gina kauyen da mayar da jama’a cikin gidanjensu na daga cikin alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na tallafa wa wadanda lamarin ya shafa, rahoton AIT.
Shettima ya ja hankalin masu zuba jari
A wani rahoton kuma Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce lokaci ya yi da za a rage dogaro da man fetur wajen bunkasa tattalin arziki
Ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da masu zuba jari, inda ya ce akwai sauran bangarori da dama da za su iya taimakawa wajen farfaɗo da tattalin arziki a Najeriya
Asali: Legit.ng