"Ba a Bangaren Fetur Kawai Ake Samun Arziki Ba," Shettima Ya ba da Shawara kan Tattali

"Ba a Bangaren Fetur Kawai Ake Samun Arziki Ba," Shettima Ya ba da Shawara kan Tattali

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce lokaci ya yi da za a rage dogaro da man fetur wajen bunkasa tattalin arziki
  • Ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da masu zuba jari, inda ya ce akwai sauran bangarori masu kyau a kasar nan
  • Mataimakin shugaban kasar ya lissafa bangarorin noma, kere-kere da makamashin zamani da wasu daga inda ya kamata a zuba jari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a zuba hannun jari a wasu bangarorin ba fetur kawai ba.

Kashim Shettima ya ce akwai bangarorin da idan aka waiwaye su, za a samu alheri mai yawa ta fuskar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Aliko Dangote ya bayyana tsawon lokacin da za a dauka wajen farfado da tattalin arziki

Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa ya bayar da shawarar rage dogaro da man fetur Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a tattauna da masu zuba hannun jari a fadar shugaban kasa Ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A sa hannun jari a noma," Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa bangaren noma da makamashin zamani na bukatar a zuba hannun jari.

Jaridar Vanguard ta a wallafa cewa Kashim Shettima ya shawarci masu zuba hannun jari su waiwayi bangaren noma da makamashin zamani da kere-kere.

Kashim Shettima ya shawarci masu zuba hannun jari su waiwayi bangaren noma da makamashin zamani da kere-kere.

Mataimakin shugaban ya kara da cewa mayar da hankali wajen bunkasa sauran bangarorin tattalin arziki na daga manufofin farfado da arzikin Najeriya na gwamnatin Tinubu.

Ya ce hakan zai taimaka sosai wajen bunkasa Najeriya ta fuskoki da dama.

Kara karanta wannan

Matashin da ya hallaka masallata a Kano ya amsa laifinsa, Kotu ta fitar da matsaya

"Cikin watanni tattalin arziki zai farfado," Dangote

A baya kun ji cewa attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya fadi lokacin da za a dauka wajen farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana haka ne bayan rantsar da majalisar duba yadda za a warware matsalar da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.