An Cafke Uban da Ya Daure Dansa Mai Shekaru 5 Cikin Sarka Ya Hana Shi Abinci
- Rundunar yan sandan Najeriya ta reshen jihar Bauchi ta cafke wani mahaifi bisa zargin cin zarafin ɗan cikinsa da ya yi
- Mahaifin mai suna Abubakar Nuhu ya shiga hannu jami'an yan sanda ne bayan wasu makwabta sun kai korafi ga jami'an tsaro
- A yayin da ake binciken Abubakar Nuhu, ya bayyanawa jami'an tsaro dalilan da suka sanya shi daure dan cikin nasa da sarka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda ta kama wani mahaifi mai suna Abubakar Nuhu da aka fi sani da Wanzam bisa cin zarafin dan Adam.
Ana zargin Abubakar Nuhu ne da daure dan cikinsa mai shekaru biyar a duniya cikin sarƙa tare da kuma azabtar da shi.
Legit ta gano labarin ne a cikin wani sako da rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano uba ya daure ɗansa
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa wata mata ce ta shiga gidan ta samu yaro mai shekaru biyar a daure cikin mummunan yanayi.
Bayan haka sai aka isar da labarin wajen mai unguwar Gwallagan Mayaka shi kuma ya isar da labarin ga rundunar yan sanda.
Dalilin daure yaro da sarƙa a Bauchi
A yayin da ake binciken mahaifin, ya bayyana cewa ya daure yaron ne mai shekaru biyar saboda yana satar kayan makwabcinsu.
Ya kuma bayyana cewa abokinsa ne ya ba shi shawarar daukan matakin domin gyara halin yaron.
Kwana uku yaro bai ci abinci ba
A yayin da yan sanda suke tambayar yaron da aka dauren, ya bayyana cewa kwanansa uku ba tare da an ba shi abinci ba.
Yaron ya kuma bayyana cewa mahaifin yana gana maza azaba a tsawon lokacin da ya yi a daure, rahoton Daily Trust.
An kama barawo a jihar Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta cafke babban ɓarawo da ake zargin ya fitini al'umma da sace-sace.
Ɓarawon da ake zargi mai suna Glory Samuel ya sace makudan kudi da kayayyaki na miliyoyin kudi daga mutane da dama a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng