“Ka da Ku Ba Coci Ko Masallaci Sadaka Daga Fansho”: Gwamna Ga Ma'aikata Masu Ritaya

“Ka da Ku Ba Coci Ko Masallaci Sadaka Daga Fansho”: Gwamna Ga Ma'aikata Masu Ritaya

  • Gwamnan jihar Lagos ya gargadi 'yan fansho kan ba da gudunmawa ga coci da masallaci daga kudin da suka samu
  • Gwamnan ya ce wannan kudi ne wanda suka sha wahala domin haka su yi amfani da shi wurin share matsalolinsu
  • Sanwo-Olu ya bayyana haka ne yayin biyan kudin 'yan fansho kusan N4.46bn a jihar ga wadanda suka yi ritaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya ba wadanda suka yi ritaya shawara yadda za su kashe kudinsu.

Sanwo-Olu ya bukaci 'yan fansho da kada su ba da kudinsu wurin gudunmawar masallatai ko coci bayan wahalar da suka sha.

Gwamna ya ba 'yan fansho shawara kan yadda za su kashe kudinsu
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shawarci 'yan fansho kan kudin da suka samu. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Getty Images

Sanwo-Olu ya ba 'yan fansho shawara

Kara karanta wannan

Alkali ya yi barazanar daure Hadimin Gwamna Abba kan shari'ar Ganduje

Gwamnan ya shawarce su da su yi amfani da kudin wurin dakile matsalolin iyalansu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka yayin biyan 'yan fanshon wanda ya kai N4.46bn a jihar ga tsofaffin ma'aikata fiye da 2,000, The Guardian ta tattaro.

"Wannan ba kudi ba ne da za ku kashe duka matsalolin iyalanku, kudinku ne wanda kuka sha wahala kuka kuma yi aiki a kansu."
"Idan suka ce za su gina coci ko masallaci suka kuma bukaci ku kawo N3m ka da ku ba su, gwamna ya gama na shi, saura naku."

- Babajide Sanwo-Olu

Gwamna Sanwo-Olu da walwalar ma'aikata

Sanwo-Olu ya kara da cewa wannan na daya daga cikin himmatuwar gwamnatinsa wurin inganta walwalar ma'aikata.

Wasu da dama sun yabawa shawarar gwamnan a kafofin sadarwa inda suka ce wasu na nan suna jiransu bayan sun fito.

Kara karanta wannan

Ana fargabar dawowar dogayen layin fetur, bashin mai ya taru a kan NNPCL

Sai dai wasu da dama sun caccaki gwamnan inda wasu ke cewa babu ruwansa da yadda mutum zai yi da kudinsa.

Gwamna Diri ya karyata zama mataimakin Atiku

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya karyata jita-jitar zama mataimakin Atiku Abubakar.

Gwamna Diri ya ce kwata-kwata ba ya bukatar zama mataimakin Atiku a zaben 2027 kamar yadda wata kungiya ta yi kira ga Atiku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.