Watanni 7 da Sakin Bam, Rundunar Sojin Najeriya Ta Zabi Tudun Biri Domin Kai Tallafi

Watanni 7 da Sakin Bam, Rundunar Sojin Najeriya Ta Zabi Tudun Biri Domin Kai Tallafi

  • Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kai tallafi ga al'ummar garin Tudun Biri da harin bom ya rista da su watanni bakwai da suka wuce
  • Manjo Janar Matirenso Saraso ya bayyana dalilin kai tallafi ga al'ummar yankin a cikin wata hira da yayi da manema labarai
  • Har ila yau, Manjo Janar Matirenso Saraso ya bayyana irin nau'in tallafin da za su kai ga mutanen Tudun Biri a wannan karon

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna- Rundunar sojin Najeriya ta ayyana Tudun Biri a cikin wuraren da za ta kai tallafin lafiya domin bikin cika shekaru 161 da kafuwa.

Garin Tudun Biri dai nan ne jirgin rundunar sojin Najeriya ya sake bom bisa kuskure a watan Disambar bara.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauyoyi sun bayyana dalilin janye jiki su bar shari'ar Aminu Ado a kotu

Tudun Biri
Sojoji za su kai tallafi Tudun Biri. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Manjo Janar Matirenso Saraso ya bayyana dalilin zaben Tudun Biri wajen kai tallafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kai tallafi Tudun Biri

Kwamandan runduna ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar Matirenso Saraso ya ce an zabi Tudun Biri ne da tallafin domin gyara alaka da ke tsakanin sojoji da mutanen garin.

Manjo Janar Matirenso Saraso ya kara da cewa hakan zai nuna cewa sojojin Najeriya suna gabatar da ayyukan jin kai ba wai yaki kawai suka iya ba.

Me za a ba mutanen Tudun Biri?

Rundunar sojin Najeriya dai ta bayyana cewa tallafin zai shafi duba marasa lafiya a garin Tudun Biri da ba su magani.

Sojoji za su duba marasa lafiya daban daban domin ba su magani kyauta da kuma ba su wasu kayan da suke buƙata domin kula da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Ana gyara gini ya ruguzowa Bayin Allah a Abuja, mutane sun samu raunuka

Kiran sojoji ga mutanen Tudun Biri

Manjo Janar Matirenso Saraso ya ce ya kamata mutanen Tudun Biri su fito kwansu da kwarkwata domin cin moriyar shirin.

Ya kuma yi kira garesu da su cigaba da ba sojojin Najeriya hadin kai domin tabbatar da tsaro a fadin Najeriya, rahoton PM News.

An fara ayyuka a Tudun Biri

A wani rahoton, kun ji cewa watanni bayan kuskuren jefa bam kan ƴan Maulidi, Malam Uba Sani ya fara cika alƙawurran da ya ɗaukar wa kauyen Tudun Biri.

A watan Disamba ne sojoji suka jefa bam kan masulmi a taron Maulidi a kauyen, lamarin da ya yi ajalin mutane sama da 150.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng