Hukumar Kwastam Ta Kama Makaman Kusan N1bn da Ake Zargin Za a Kai Ga ’Yan Ta’adda
- Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da sake cakfe tarin makamai da ake ƙoƙarin shigowa da su Najeriya ta barauniyar hanya
- Shugaban hukumar, Adewale Adeniyi ya tabbatar da cewa a ranar Laraba, 3 ga watan Yuli suka sake cafke makaman a jihar Legas
- Kama makaman na zuwa ne kwanaki kadan bayan cafke tarin makamai da hukumar ta yi ana ƙoƙarin shigowa da su Najeriya daga Turkiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Hukumar kwastam ta sake cafke wasu rukunin makamai da ake kokarin shigowa da su Najeriya.
Nasarar da hukumar ta samu ya biyo bayan kama wasu makaman da ta yi ne a ranar Litinin da ta wuce.
Legit ta gano lamarin ne a cikin wani sako da hukumar kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makaman da kwastam ta kama a Legas
Hukumar kwastam ta tabbatar da cewa ta kama bindigogi guda 55 da aka boye cikin manyan kwalaye hudu.
Hukumar ta kuma kama hular kwano, rigunan soja da sauran makaman da kuɗinsu zai haura Naira biliyan 1.
Ana zargin daga Turkiyya ake turo makaman
Shugaban hukumar kwastam Adewale Adeniyi ya ce yana zargin cewa akwai wasu miyagu 'yan Najeriya da suke turo makamai daga Turkiyya.
Adewale Adeniyi ya ce akwai alamar cewa mutanen sun fake a Turkiyya suna turo makamai Najeriya domin taimakon yan ta'adda.
Kwastam za ta cigaba da ƙoƙari Inji Shugabanta
Adewale Adeniyi ya ce jami'an kwastam za su cigaba da saka ido a dukkan iyakokin Najeriya domin dakile yunkurin shigo da makamai.
Ya kuma jinjinawa jami'an kwastam sa suka ta kokari wajen kama kayan da miyagu ke kokarin shigowa da su Najeriya.
Hukumar kwastam na kokarin sauke farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta kasa ta yi alwashin kawo karshen matsalar boye abinci da ta addabi daukacin al'ummar Najeriya.
Kwastam ta ce a yanzu haka ta dauki masu matakai wanda za su kawo karshen matsalar domin kawo saukin rayuwa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng