"Bashi Mai Sharudan Shaidanci": Shehu Sani Ya Magantu Kan Yarjejejniyar Samoa

"Bashi Mai Sharudan Shaidanci": Shehu Sani Ya Magantu Kan Yarjejejniyar Samoa

  • Ana ta sukar Shugaba Bola Tinibu kan yarjejeniyar Samoa wadda gwamnatin Najeriya da wasu kasashen Afrika suka sawa hannu
  • Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya bayyana damuwa kan sharuddan dake tattare da bashin $150bn da ke kunshe a yarjejeniyar
  • Sanata Shehu Sani yayi kira da Tinubu da sauran shugabannin Afrika da su gujewa lamunin mai "sharuddan shaidanci"

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, yayin kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye daga yarjejeniyar Samoa da yasa hannu.

An gano cewa shugaban kasar ya saka hannu kan wannan yarjejeniyar tun ranar 15 ga Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Shinkafi ya fadi abin da ke kawo rashin tsaro a Arewa maso Yamma, ya ba da mafita

"Lamuni mai sharuddan shaidanci": Shehu Sani ya magantu kan Samoa. Hoto daga Sanata Shehu Sani, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
"Bashi mai sharuddan shaidanci": Shehu Sani ya magantu kan yarjejejniyar Samoa
Asali: Facebook

A wani martanin gaggawa kan wannan batu, Shahu Sani ya ja kunne kasashen Afrika kan yarjejeniyar Samoa ya kira mai dauke da "sharuddan shaidanci" a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni dai sun bayyana cewa cece-kuce ya lullube lamunin dala biliyan 150 da ke kunshe a yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayyar Najeriya tasa hannu da kungiyar EU.

Gwamnati ta musanta batun auren jinsi

Amma a ranar Alhamis, 4 ga watan Yulin 2024, gwamnatin tarayya ta musanta rahoton amincewa da hakkokin 'yan luwadi, 'yan madigo da masu sauya jinsi a yarjejeniyar.

Mun ruwaito cewa Mohammed Idris, ministan yada labarai ya ce Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar ne bayan ta kiyaye dokokin kasarta.

Mista Idris ya bayyana cewa, dokar Najeriya kan haramcin auren jinsi ta girmi wannan yarjejeniyar don haka ba wani abu ne da zai daga hankalin 'yan kasar ba.

Kara karanta wannan

"Dokar haramta auren jinsi ta girmi yarjejeniyar Samoa" Gwamnati ta yi karin haske

Shehu Sani ya magantu kan Samoa

Sai dai duk da hakan, Sanata Shehu Sani ya yi kira ga Tinubu da sauran shugabannin Afrika da suka amince da Samoa da su koma tare da warware yarjejeniyar.

Sanata Sani ya wallafa cewa:

"Kada kasashen Afrika su amince su karbi bashi ko tallafi daga kowacce kasa, kungiyoyin kasashe ko cibiyoyin kasa da kasa matukar sun zo da sharuddan shaidanci da suka ci karo da al'adu, addinai da tsarikanmu.
"Akwai bukatar dukkanin kasashen Afrika har da Najeriya, su koma tare da janye amincewarsu ga yarjejeniyar Samoa."

Kalli sakon sanatan a kasa:

An soki gwamnati kan yarjejeniyar Samoa

Tun da fari, mun ruwaito cewa sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta yi ya jawo cece kuce, inda wasu ke ganin ana so a shigo da wani sabon al'amari Najeriya.

Wasu malaman addini da kungiyoyin fafutuka sun fusata kan sanya hannu a yarjejeniyar Samoa wadda ake fargabar za ta iya ba masu auren jinsi 'yanci a cikin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel