NCAA Ta Fitar da Jerin Jiragen Sama 10 da Gwamnatin Tinubu Ta Hana Tashi a Najeriya

NCAA Ta Fitar da Jerin Jiragen Sama 10 da Gwamnatin Tinubu Ta Hana Tashi a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta dauki mataki mai tsauri kan wasu kamfanonin jiragen sama saboda saɓawa dokokin sufurin jirage a Najeriya
  • Hukumar lura da zirga zirgar jiragen sama ta kasa (NCAA) ta dauki matakin tare da bayyana dalilan dakatar da kamfanonin jiragen daga aiki
  • NCAA ta kuma bayyana matakin da za ta cigaba da dauka kan dukkan kamfanin jirgin saman da aka samu ya saɓa dokar sufurin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukumar NCAA ta dauki mataki mai tsauri kan wasu kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu.

NCAA ta tabbatar da kwace lasisin kamfanonin jiragen bisa karya dokokin aiki da suka rattaba hannu a kai.

Kara karanta wannan

Jerin makamai da kwastam ta kama ana shirin shigowa da su Najeriya cikin shekaru 7

Jirgin sama
Hukumar NCAA ta dakatar da jirage daga aiki a Najeriya. (An yi mafani da hoton ne domin buga misalai) Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kamfanoni guda 10 hukumar NCAA ta dakatar bisa saba dokoki sufuri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin dakatar da jiragen sama daga tashi

Hukumar kula da zirgar zirgar jiragen saman Najeriya (NCAA) ta ce ta dakatar da kamfanonin ne bisa gaza sabunta rajista da ya kamata su yi tun ranar 19 ga Afrilu.

NCAA ta kuma zargi kamfanoni da saɓa ƙa'idar aiki wajen daukar fasinja bayan ba su da hurumin yin haka.

Kamfanonin jiragen da aka dakatarwa zirga zirga

Jaridar Tribune ta ruwato cewa hukumar NCAA ta ayyana kamfanonin da suka saɓa dokar aiki kamar haka:

  1. Azikel Dredging Nigeria Ltd
  2. Bli-Aviation Safety Services
  3. Ferry Aviation Developments Ltd
  4. Matrix Energy Ltd
  5. Marrietta Management Services Ltd
  6. Worldwide Skypaths Services
  7. Mattini Airline Services Ltd
  8. Aero Lead Ltd
  9. Sky Bird Air Ltd
  10. Ezuma Jets Ltd.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama ɗan damfara da ya karbi N4.5m domin samar da kujerun Hajji

NCAA za ta cigaba da ɗaukan mataki

Hukumar NCAA ta ce za ta cigaba da dukan mataki kan dukkan kamfanin da ya saɓawa dokar sufuri a Najeriya domin tabbatar da tsaro.

Hukumar ta ce tuni ta baza jami'anta a filayen jiragen saman Najeriya domin tabbatar da cewa jirage da aka dakatar ba sa aiki.

An kirkiro masu kula da filin jiragen sama

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta kirkiro sababbin jami'ai domin magance matsalolin tsaro a manyan filayen jiragen sama.

An kaddamar da sababbin jami'an tsaron ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Janar Murtala Muhammad a birnin Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel