EFCC Ta Fallasa Tsohon Gwamna, Tsofafffin Ministocin da Ke Shirya Mata Makarkashiya

EFCC Ta Fallasa Tsohon Gwamna, Tsofafffin Ministocin da Ke Shirya Mata Makarkashiya

  • Hukumar EFCC ta yi ƙarin haske kan zanga-zangar da ta yi zargin wasu na shiryawa domin nuna adawa da ayyukanta
  • Kakakin hukumar ya bayyana cewa wani tsohon gwamna da wasu tsofaffin ministoci biyu ne ke da hannu a shirya zanga-zangar
  • Dele Oyewale ya bayyana cewa duk da zanga-zangar da ake son yi, jami'an hukumar ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayyana masu hannu a zanga-zangar da ake shirin yi domin nuna adawa da ayyukanta.

Hukumar EFCC ta ce wani tsohon gwamna da wasu tsofaffin ministoci biyu ne ke da hannu a zanga-zangar da ake shirin shiryawa.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado makarkashiyar da ake kulla mata, hukumar ta aika da gargadi

EFCC ta fadi masu hannu a zanga-zangar da ake shirya mata
EFCC ta fadi masu hannu kan zanga-zangar da ake shiryawa a kanta Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Facebook

EFCC ta ce duk da zanga-zangar da aka shirya, jami’anta za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da wani shakku ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me EFCC ta ce kan zanga-zanga?

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen ƴan jarida a yayin wani taron manema labarai a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Da yake amsa tambaya kan babban abin da ya janyo zanga-zangar da aka shirya yi, Dele Oyewale ya ce saboda ayyukan hukumar na shafar wasu masu wawurar dukiyar ƙasa ne, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Gaba ɗaya dukkanin waɗannan mutanen masu maganar a kawo ƙarshen EFCC, kada a kawo ƙarshen EFCC, a ruguza EFCC, ka da a ruguza EFCC, mutane ne waɗanda ayyukan hukumar ke shafa."
"Idan akwai hukuma irin EFCC, kuma ba a yi mata irin wannan sukar, hakan na nufin ko dai ba mu yin aikin da ya dace ko jama'a ba su damu da abin da muke yi ba."

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya dokar zaman gida ta tsawon sa'o'i 24 a ƙaramar hukumar Ukum

"Saboda haka, mun san cewa tabbas ayyukanmu suna shafar mutanen da ba su da gaskiya, kuma muna sane da cewa dole ne za su so su yaƙe mu."

- Dele Oyewale

Jami'in EFCC ya kashe kansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami’in hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ya yanke shawarar barin duniya.

Jami'in na hukumar EFCC ya salwantar da ransa ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel