“Dokar Haramta Auren Jinsi Ta Girmi Yarjejeniyar Samoa” Gwamnati Ta Yi Karin Haske
- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, dokarta ta haramta auren jinsi a Najeriya ta girmi sa hannu kan yarjejeniyar Samoa
- Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya sanar da cewa jami'an Najeriya sun kiyaye tsaf kafin saka hannu kan yarjejeniyar
- Ya ce kasantuwar Najeriya ƙasa mai doka yasa gwamnatin Tinubu ba za ta sa hannu kan abinda ya saɓa ra'ayin 'yan ƙasa ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar da sa hannu kan yarjejeniyar Samoa, inda tace dokarta kan auren jinsi ta rigayi yarjejeniyar.
Yarjejeniyar Samoa haɗin gwiwa ne tsakanin kungiyar kasashen Turai da kuma kasashen Afrika da ke cikin kungiyar OACPS.
An fara tattaunawa kan yarjejeniyar ne a shekarar 2018, a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73 kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan da gwamnati ta sanar da cewa za ta sanya hannu kan yarjejeniyar ake ta cece kuce, inda wasu malamai da masu rajin kare haƙƙin bil adama suke sukar gwamnati.
Najeriya ta kiyaye dokokinta kan Samoa
Amma a wata takarda da aka fitar a daren Alhamis, Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai, ya bayar da ƙarin bayani kan yarjejeniyar, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya nuna.
Ministan ya ce:
“A ranar 28 ga Yuni, 2024, Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa a sakatariyar kungiyar kasashen Afirka, Caribbean, da Pacific (OACPS) a Brussels, Belgium.
“Yarjejeniyar tana da maƙalu 103 da ta haɗa da na Afirika - EU, Caribbean-EU, da Fasha-EU, inda kowanne yake bayani kan matsalolin yankin."
"Ya zama dole a tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kasancewarta mai aiki da doka, ba za ta shiga wata yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ba da za ta saɓa ra'ayin ƙasa da 'yan ƙasar ba.
"Muhimmancin yarjejeniyar Samoa" - Gwamnati
Sanarwar ministan ta ci gaba da cewa:
"A yayin tattaunawa kan yarjejeniyar, jami'anmu sun kiyaye duka wasu haƙƙoƙi a tsarin tsakanin EU da OACPS, kuma dokarmu ta haramta auren jinsi ta 2014 ta rigayi wannan yarjejeniya.
“Yarjejeniyar Samoa ba komai bace face tsarin haɗin kai na shari'a tsakanin OACPS da EU, wanda zai taimaka wajen inganta cigaba mai ɗorewa.
Yarjejeniyar za ta taimaka wajen yaƙar sauyin yanayi da illolinsa, samar da damarmaakin saka hannayen jari da assasa haɗaka tsakanin ƙasashen OACPS."
Dan majalisar Kano ta magantu kan Samoa
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar da ke wakiltar Takai/Sumaila, Hon. Rabiu Yusuf, ya ce Najeriya na iya saka hannu kan yarjejeniyar Samoa idan aka cire bangaren auren jinsi.
Dan majalisar wakilan ya lura cewa yarjejeniyar Samoa tana da fa'ida ga Najeriya, don haka akwai bukatar a dauki kasadar amincewa da ita amma a kafa sharadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng