Auren jinsi a garin Kano: Wata Budurwa ta haka ma wasu yan Mata ramin mugunta, amma ta fada

Auren jinsi a garin Kano: Wata Budurwa ta haka ma wasu yan Mata ramin mugunta, amma ta fada

Hukumar kula da da’a da kuma daidaita sahun al’umma ta jihar Kano, wato Hisbah a karkashin jagorancin Malam Aminu Daurawa ta sanar da wanke wasu yan mata biyu da ake zargi da aikata Madigo da har ta kais u ga auren kansu.

Legit.ng ta ruwaito a kwanakin baya ne hukumar ta kaddamar da bincike akan yan matan biyu, masu sunaye kamar haka; Fatima da Rukayya, sakamakon tsegumi da wata kawarsu ta kai ma hukumar, inda ta ce sun yi auren jinsi daya.

KU KARANTA: Siyasar Kano: Kwamishinan Ganduje ya dauki alwashin tika Kwankwaso da kasa

Auren jinsi a garin Kano: Wata Budurwa ta haka ma wasu yan Mata ramin mugunta, amma ta fada

Fatima da Rukayya

Sai dai bayan kammala cikakken bincike na kwakwaf, tare da bin diddigi, Hisbah ta wanke yan Matan, inda a yanzu haka kaikayi ya koma kan mashekiya, inda jami’an hukumar Hisbah suka yi ram da kawar da ta kulla musu wannan sharri.

Daga karshe sanarwar ta kara da cewa kazafin da kawar Fatima da Rukayya ta yi musu babban laifi ne, kuma za ta girbi abinda ta shuka kamar yadda shari’a ta tanadar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel