1446AH: Gwamnati Ta Ba da Hutu Domin Zuwan Sabuwar Shekarar Musulunci

1446AH: Gwamnati Ta Ba da Hutu Domin Zuwan Sabuwar Shekarar Musulunci

  • Gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, ta ayyana ranar Litinin, ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai wanda ya sanar da hakan ya bayyana cewa an ba da hutun ne domin zuwan sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH
  • Ya buƙaci al'ummar jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu'oi domin samun zaman lafiya da ci gaba a jihar da ƙasa baki ɗaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar.

Gwamnatin ta ayyana ranar ne a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar shekarar musulunci ta 1446 bayan Hijirah.

Kara karanta wannan

An kai harin kunar bakin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja? Gaskiya ta bayyana

Gwamnatin Oyo ta ba da hutu a jihar
Gwamnatin Oyo ta ba da hutu saboda zuwan sabuwar shekarar musulunci Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Gwamnatin Oyo ta ba da hutun shekarar musulunci

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Prince Dotun Oyelade, ya fitar a ranar Alhamis, 4 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fahimci muhimmancin da shekarar musuluncin take da shi a rayuwar musulman jihar.

Ya yi kira ga mutanen jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu'o'in samun zaman lafiya da ci gaba a jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya.

Kwamishinan ya kuma buƙaci jama'a da su koyi da abin da ranar take koyarwa tare da haɗa kai domin zama ƴan uwan juna.

Shekarar musulunci: Jawabin gwamnatin jihar Oyo

"An ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yulin 2024 matsayin ranar hutu domin zuwan lokacin Hijirah, wanda yake nuna Hijirar da Annabi Muhammad (SAW) ya yi daga Makkah zuwa Madina a shekarar 622AD."

Kara karanta wannan

Borno: Majalisar dattawa ta faɗi sakacin da ya jawo aka kai harin bam a Gwoza

"Hijirah lokaci ne na yin tunani, addu'a da son juna. Mu taru a wannan rana domin yin addu'ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a jihar mu da ƙasar mu."

- Prince Dotun Oyelade

Gwamna Makinde ya yi garambawul

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi wani ɗan karamin garambawul a majalisar zartaswan jiharsa.

Gwamna Seyi Makinde ya sauyawa wasu kwamishinoni wuraren aiki domin inganta ayyukan gwamnatinsa da kuma ƙoƙarin cika muradan al'ummar jihar Oyo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel