Binuwai: 'Yan Sanda Sun Cafke Matasan da Suka Tada Hankula da Sunan Zanga Zanga

Binuwai: 'Yan Sanda Sun Cafke Matasan da Suka Tada Hankula da Sunan Zanga Zanga

  • Rundunar 'yan sandan jihar Binuwai ta cafke wasu matasa da ake zargi da tayar da hankula yayin zanga-zanga da ya gudana a Ukum
  • Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, SP Catherine Anene ta ce wannan mataki ne na wanzar da zaman lafiya a karamar hukumar ta Ukum
  • Mazauna yankin sun gudanar da zanga-zanga bayan wani mummunan hari da ya salwantar da rayukan mutane 11 da safiyar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue- 'Yan sanda a jihar Binuwai sun kama wasu matasa da ake zargi da kone-kone yayin zanga-zanga da aka gudanar ranar Laraba a jihar.

Matasan karamar hukumar Ukum sun gudanar da zanga zanga saboda yawan kashe su da 'yan ta'adda ke yi babu kakkautawa a yankin.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Kashen-kashen jama'an Binuwai ya jawo zanga zanga ta barke

Benue State Government
An kama wadanda ake zargi da tayar da hankula lokacin zanga zanga a Binuwai Hoto: Benue State Government
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar 'yan sandan jihar ta tabbayar da kama matasa 18 da ake zargi da sa hannunsu aka rika kone-kone yayin zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan yan sanda ya koma Ukum

Bayan cafke wasu matasa da ake zargi da kokarin tayar da zaune tsaye ranar Laraba yayin zanga-zanga kan ta'addanci, rundunar 'yan sanda ta dauki wasu matakan wanzar da zaman lafiya.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundnar, SP Catherine Anene ta shaidawa manema labarai a Makurdi cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Hassan Yabanet ya koma karamar hukumar.

Matasan sun gudanar da zanga-zanga ne bayan kashe mutane 11 da 'yan ta'adda su ka yi, amma lamarin ya rikide zuwa tashin hankali.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa yanzu haka an sanya dokar ta baci na awanni 24 a yankin domin dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama shugaban 'yan banga dauke da sassan jikin ɗan Adam

Binuwai: Ana zanga zanga saboda ta'addanci

A wani labarin kun ji cewa matasa a karamar hukumar Ukum da ke jihar Binuwai sun gudanar da zanga-zanga kan harin ta'adanci.

A safiyar Laraba ne wasu 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar tare da kashe mutane da dama, lamarin da mutanen su ka ce ya ishe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel