Komai ya Tsaya Cak, Mamakon Ruwan Sama ya Wanke Unguwanni a Legas
- Legas ta gamu da mamakon ruwan sama da aka shafe awanni ana yi, yayin da hakan ya dakatar da ayyuka a sassan jihar
- Rahotanni sun bayyana cewa mamakon ruwan ya shanye tituna tare da ruguzo da gidaje da dama, a lokaci guda kuma an rufe shaguna
- Dama a baya hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) ta yi jan kunnen cewa akwai yiwuwar mummunan ambaliyar ruwa a sassan kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos- Bayan jan kunne da hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) ta yi kan barkewar ambaliyar ruwa a Najeriya, a jiya ruwa ya mamaye jihar Legas.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta yiwa wasu 'yan Najeriya gata, an dakatar da karbar haraji daga garesu
Mamakon ruwan saman ya haddasa cunkosun ababen hawa yayin da hada-hada ta tsaya cak a yankuna da dama na jihar.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa ruwan kamar da bakin kwarya ya raba mazauna Ibeju-Lekki da muhallansu, yayin da kowa ke neman mafaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje
Ruwa kamar da bakin kwarya na aka yi a Legas na akalla awa 10 ya rusa gidaje da dama yayin da ruwan mamaye titunan jihar.
Jaridar Punch ta wallafa cewa mamakon ruwan ya rikito da gini mai hawa biyu a Mushin, yayin da dalibai su ka gaza zuwa makarantu.
A hukumance, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa an shafe awa tara ana ruwan, sai dai wasu na ganin an shafe awanni 12 ana ruwan a yankunansu.
Wasu daga yankunan da lamarinya fi kamari sun hada da Iyana-Oworo, Agege, Ijegun-Isheri Osun, Gbagada, Lagos Island, Eredo, Bojije, Epe, Sangotedo, Ibeju-Lekki, Awoyaya, Labora da Abijon.
Ruwa ya rusa gidaje 100 a Filato
A wani labarin, kun ji cewa mamakon ruwan sama ya lalata gidaje sama da 100 a jihar Filato, inda mutane suka rasa matsugunasu a wasu yankunan.
Ruwan, wanda ya fi karfi a kananan hukumomin Jos ta Arewa da ta Kudu ya lalata rufin kwanon wasu gidajen, yayin da wasu kuma kofofin ne suka fita.
Asali: Legit.ng