Borno: Majalisar Dattawa Ta Faɗi Sakacin da Ya Jawo Aka Kai Harin Bam a Gwoza

Borno: Majalisar Dattawa Ta Faɗi Sakacin da Ya Jawo Aka Kai Harin Bam a Gwoza

  • Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta umarci sojoji su sauya salon yaƙi da ƴan tada kayar baya a Najeriya
  • A zaman ranar Laraba, 3 ga watan Yuli, majalisar ta ɗora alhakin harin bam da aka kai a Gwoza kan sakacin tattara bayanan sirri
  • Ta ce lokaci ya yi da jami'an tsaron za su shigo zamani, su fara amfani da dabarun kimiyya da fasaha wajen kakkaɓe miyagu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar dattawa ta dora alhakin harin kunar bakin wake da aka kai a garin Gwoza na jihar Borno a kan gaza tattara bayanan sirri daga bangaren jami’an tsaro.

Shugaban majalisar Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a yayin muhawara kan kudirin da mai tsawatarwa Sanata Ali Ndume, ya gabatar a zaman ranar Laraba, 3 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Hargitsi ya tashi a majalisar wakilai yayin da aka zargi mataimakin kakaki da nuna bambanci

Majalisar dattawan Najeriya.
Majalisar dattawa ta ɗora alhakin harin bam da aka kai a Gwoza kan sakacin tattara bayanan sirri Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Tun farko a jawabinsa, Ndume ya ce har yanzun ƴan ta'adda na da mafaka a tsaunin Mandara, dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattijai ta kawo mafita

A matakan da ta ɗauka kan kudirin, majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta umurci sojoji su sake lalubo dabarun yaƙi da ƴan tada ƙayar baya.

Ta bukaci dakarun sojoji su canza dabarun tunkarar ƴan ta'adda, su koma amfani da fasahar zamani da dabarun kimiyya domin tabbatar da zaman lafiya.

Sanatocin sun lura cewa dogaro da hanyoyin da kowa ya sani wajen tunkarar ƴan tayar da ƙayar baya kamar tura dakarun sojoji ba kasafai ake samun nasara ba.

Zallar karfin sojoji zai murkushe 'yan ta'adda?

A cewar majalisar dattawan, tsayawa kan waɗannan hanyoyi na karfin soji kaɗai na ci gaba da bai wa ƴan ta'adda damar ɓullo da wasu hanyoyin da ba a yi zato ba a yanzu.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta binciki tashin bam a Borno, ta dora laifin kan jama'ar yankin

Ta ce hakan na jawo asarar rayukan ƴan Najeriya da dukiyoyinsu, wanda ya kamata hukumomin tsaro su taka wa lamarin birki, Premium Times ta tattaro.

Tinubu ya naɗa mace shugabaci FGSHLB

A wani rahoton, Bola Tinubu ya amince da naɗin Hajiya Salamatu Ladi Ahmed a matsayin sabuwar babbar sakatariyar hukumar ba da lamuni ta FGSHLB.

Shugaban ƙasar ya tabbatar da wannan naɗi ne ta hannun shugabar ma'aikatan tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan ranar Talata a birnin Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel