'Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yan Gudun Hijira Bayan Sun Raba Su da Gidajensu

'Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yan Gudun Hijira Bayan Sun Raba Su da Gidajensu

  • An samu asarar rayuka a jihar Benue bayan ƴan bindiga sun farmaki wasu ƴan gudun hijira da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun hallaka ƴan gudun hijiran mutum uku lokacin da suke dawowa daga gona a ranar Litinin
  • An binne gawarwakin mutum biyu daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka kashe yayin da aka ajiye ɗaya gawar a wani ɗakin ajiye gawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne ɗauke da makamai sun kashe mutane uku a jihar Benue.

Mutanen dai waɗanda ke rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira na Agagbe sun rasa rayukansu ne lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka a rikicin manoma da makiya a jihar Jigawa

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Benue
'Yan bindiga sun hallaka 'yan gudun hijira a Benue Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun hallaka mutane a Benue

Ƴan bindigan sun hallaka mutanen ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da suke dawowa daga gona.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban sansanin ƴan gudun hijiran, Terna Jacob, ya tabbatarwa da wakilin jaridar The Punch aukuwar lamarin a ranar Talata.

"Sun rasa rayukansu ne yayin da suke dawowa daga gona zuwa makwancinsu a garin Agagbe domin makiyaya sun ƙona musu gidajensu."

- Terna Jacob

Ya bayyana sunayensu a matsayin Mista Ameeya Solomom mai shekara 38 na ƙauyen Tse Kuan a gundumar Mbabuande, Adagu Terwase mai shekara 40 na ƙauyen Tse Abu da Orkaha Terkende mai shekara 16 na ƙauyen Tse Maihwa.

Jaridar Daily Trust ta ce an binne biyu daga cikin waɗanda suka mutu yayin da aka ajiye gawar mutum na ukun a ɗakin ajiye gawa na Agagbe.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a wani hari a jihar Katsina

Legit Hausa tuntubi jami’ar hulɗa da jama’a ta ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, wacce ta ce ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.

"Ban samu rahoton faruwar lamarin ba."

- SP Catherine Anene

Ƴan bindiga sun hallaka manoma

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka wasu manoma mutum huɗu yayin da suke aiki a gonakinsu a wani harin ta'addanci a jihar Katsina.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutanen ne a ƙaramar hukumar Jibia mai fama da matsalar rashin tsaro a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng