Ta'addanci: Kashen Kashen Jama'an Binuwai ya Jawo Zanga Zanga Ta Barke
- A safiyar yau wasu 'yan ta'adda su ka kai mumunan hari kan mazauna garin Ayati a jihar Binuwai tare da kashe mutane 11
- Matasan yankin sun fusata saboda harin sanyin safiyar Larabar nan, inda su ka gudanar da zanga zanga domin nuna takaicinsu
- Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun fasa abubuwa da dama a shelkwatar karamar hukumar Ukum da duwatsu da sanduna
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Benue- Mazauna jihar Binuwai sun fara zanga-zanga saboda karuwar hare-haren 'yan ta'adda da ke salwantar da rayukan jama'a.
A safiyar yau ne 'yan ta'adda su ka kai hari garin Ayati a karamar hukumar Ukum inda su ka kashe mutane 11 ba haira ba dalili.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Ukum na daga cikin kananan hukumomi uku a jihar Binuwai da 'yan ta'adda su ka raina, inda su ke kai hare-hare yadda su ka ga dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan Ukum sun fusata a Binuwai
Matasa da sauran mazauna karamar hukumar Ukum sun fusata da kisan mutane 11 da 'yan bindiga su ka yi a safiyar yau Laraba.
Fusatattun matasan sun durfafi shelkwatar mazabar Borikyo inda su ka bayyana rashin jin dadinsu ta hanyar zanga-zanga domin nuna damuwarsu.
Zanga-zanga ya barke a jihar Binuwai
Rahotanni sun ce matasan sun yi dafifi kan titin Sankera-Ayati saboda rashin kwanciyar hankalin da ya addabe su, kamar yadda Jaridar Punch ta wallafa.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun farfasa wasu kayayyaki a sakatariyar karamar hukumar, inda suka fasa taga da duwatsu da sanduna.
'Yan sanda sun ragargaji miyagu a Binuwai
A baya mun kawo labarin cewa jami'an yan sanda sun yi bajinta wajen kai hari maboyar 'yan ta'adda tare da kashe biyu daga cikin miyagun da su ka addabi jama'a.
An yi nasara kan 'yan ta'addan ne bayan jami'an tsaro sun kai hari sansanin miyagun da ke a gundumar Mbatyula cikin karamar hukumar Katsina-Ala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng