Yan Sanda Sun Kama Shugaban ’Yan Banga Dauke da Sassan Jikin Ɗan Adam
- Rundunar yan sanda a jihar Rivers ta yi nasarar cafke wani shugaban yan banga dauke da sassan daban-daban na jikin ɗan Adam
- Yan sanda sun kama shugaban mai suna Felix Nwaobakata a wani wuri da ya buya a yankin Omoku a karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni
- Haka zalika rundunar ta kai farmaki kan wasu yan banga a yankin inda ta kama wasu da ake zargi da aikata manyan laifuffuka a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Rundunar yan sanda a jihar Rivers ta kama wani shugaban yan banga dauke da sassan jikin ɗan Adam.
Biyo bayan kama shugaban mai suna Felix Nwaobakata, rundunar ta kara kai samame kan wasu yan banga a yankin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama Felix Nwaobakata ne a karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni ta jihar Rivers.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama shugaban yan banga
Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama Felix Nwaobakata dauke da ƙoƙon kan dan Adam guda biyu, rahoton Leadership.
Bayan haka rundunar ta tabbatar da samun Felix Nwaobakata da ƙashin dan Adam a maboyarsa da ke Omoku.
Yadda aka kama shugaban yan banga
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa a ranar 9 ga watan Mayu ta samu korafi a kan garkuwa da mutane da ke zargin yan banga ne suka yi.
Saboda haka sai rundunar ta tura gayyata ga yan banga karkashin Felix Nwaobakata amma sai suka ki amsa gayyatar kuma suka yi yunkurin kai hari ga yan sanda.
Biyo bayan haka ne rundunar yan sanda ta tsananta bincike har ta gano maboyar Felix Nwaobakata ta kuma cafke shi.
An zargi jagoran banga da kisan kai
Kakakin yan sanda a jihar Rivers Grace Iringe-Koko ta ce ana zargin Felix da kisan wasu mutane biyu a ranar 1 ga watan Yuli.
Grace Iringe-Koko ta ce Felix ya kama mutanen tare da kwace musu babur yana ikirarin cewa su masu garkuwa da mutane ne.
Yan sanda sun yi mamaya a Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sanda sun tsare duka kofofin zuwa gidajen ‘yan majalisu na jihar Rivers.
An gano cewa tun bayan da gwamnan jihar, Simi Fubara ya kai ziyara bangaren gidajen ne 'yan majalisar adawa ke ta da jijiyoyin wuya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng