Majalisar Dokokin Kano ta Musanta Fargabar Harin Bam Ya Hana Zama Bayan Tsige Sarakuna

Majalisar Dokokin Kano ta Musanta Fargabar Harin Bam Ya Hana Zama Bayan Tsige Sarakuna

  • Majalisar dokokin Kano ta musanta cewa ta na fargabar za a kai mata hari saboda dokar rushe masarautun biyar da Abdullahi Ganduje ya kirkira
  • A sanarwar da mai magana da yawun shugaban majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, ya ce labarin ba shi da tushe ballantana makama
  • Tun dai bayan tabbatar da dokar rushe masarautun Kano ne majalisar dokokin jihar ta dakatar da zama, amma ta ce za ta dawo ranar 15 ga Yuli 2024

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Majalisar dokokin Kano ta musanta cewa tsoron za a iya kawo masu hari saboda rikicin masarautar Kano ne ya sa ta ki zama.

Kara karanta wannan

NIN: Majalisar dattawa na kokarin kawo dokar da za ta shafi yan ƙasashen waje

Idan za a iya tunawa, majalisar ta amince da dokar da ta rushe masarautun Kano biyar, tare da sahalewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gaggauta nada sabon Sarki.

majalisa
Majalisar dokokin Kano ta musanta cewa ta dakatar da zama saboda tsoron hari Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa a sanarwar da mai magana da yawun shugaban majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, ya musanta cewa tsoro ne ya hana zaman majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan samar da wancan doka ne dai 'yan majalisar suka tafi hutu, wanda har yanzu ba su ci gaba da zama ba.

"Majalisar Kano za ta cigaba da zama," Shawai

Kamaluddeen Sani Shawai, mai magana da yawun shugaban majalisar dokokin Kano, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ya bayyana rahoton cewa tsoro ya hana zaman majalisa da aikin magauta.

Ya bayyana haka ne a sanarwar da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce 'yan majalisa sun je su huta ne, amma za su dawo zama ranar 15 Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 3 da aka samu sabani tsakanin sababbin gwamnoni da sarakunan gargajiya

A baya, Jaridar Premium Times ta wallafa cewa 'yan majalisar na fargabar ko za a kai masu hari saboda dokar masarauta da ya jawo rushe masarautu.

"Majalisa na da yancin hutu" Inji Falgore

A zantawarsa da Legit Hausa ta wayar tarho, mai magana da yawun shugaban majalisar dokokin Kano, Kamaluddeen Sani Shawai ya ce majalisa na da 'yancin tafiya hutu. Shawai ya ce bayan hutun da majalisa ta yi gabanin sallah babba, sun ji jita-jita cewa tsoron kai masu hari ne ya su kin ci gaba da zama, amma batun ba haka ba ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta mayar da martani kan ɗaga tuta a fadar da Aminu Ado ke zaune

Majalisar Kano ta rusa nadin sarakuna

A baya mun ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kano ta rusa daukkanin sarakuna biyar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta nada a 2019.

Majalisar ta dauki matakin ne a ranar Alhamis, inda ta ba gwamna Abba Kabir Yusuf ikon ya gaggauta kiran masu nada sarki a nada sabon sarki a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.