Ana Kukan Tsadar Rayuwa, Kamfanin KAEDCO Ya Kara Kudin Shan Wutar Lantarki

Ana Kukan Tsadar Rayuwa, Kamfanin KAEDCO Ya Kara Kudin Shan Wutar Lantarki

  • Wata sanarwa da Legit Hausa ta ci karo da ita na nuni da cewa kamfanin rarraba lantarki na KAEDCO ya yi karin kudin wuta
  • KAEDCO ya sanar da cewa ya yi karin kudin wuta ga abokan huldarsa da ke kan tsarin 'band A' daga N206.80/kwh zuwa N209.5/kwh
  • Kamfanin rarraba wutan ya kara da cewa karin kudin wutar bai shafi abokan hulda da ke kan tsarin 'band B, C, D da kuma E' ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - A yau Laraba kamfanin rarraba lantarkin Kaduna (KAEDCO) ya sanar da karin kudin wuta ga abokan huldarsa da ke kan tsarin 'band A' daga N206.80/kwh zuwa N209.5/kwh.

Kara karanta wannan

"A koma salon mulkinsu Sardauna": An fadawa Tinubu hanyar magance matsalolin Najeriya

"Hukumar kamfanin rarraba lantarkin Kaduna na sanar da jama'a cewa an sake kara kuɗin wuta ga 'Band A' daga N206.80/kwh zuwa N209.5kwh," in ji wata sanarwa.

Kamfanin KAEDCO ya sanar da karin kudin wutar lantarki
Kamfanin KAEDCO ya kara kudin wutar lantarki daga N206.80/kwh zuwa N209.5/kwh. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

"Dalilin yin karin kudin wuta" - KAEDCO

Wannan sanarwar dai na dauke ne da sa hannun shugaban sashen sadarwa na kamfanin, Abdulazeez Abdullahi wadda KAEDCO ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce wannan karin kudin ya fara aiki ne a ranar 1 ga Yuli, 2024, amma an fitar da sanarwar karin a ranar 3 ga Yuli, 2024.

Kamfanin ya ba wa abokan huldarsa tabbacin ci gaba da samar da wutar lantarki na sa'o'i 20 zuwa 24 a kowace rana kamar yadda aka tsara a cikin tsarin bayar da wutar.

Wadanda karin kudin wuta ya shafa

Kamfanin rarraba wutar na Kaduna ya kara da cewa karin kudin wutar lantarkin bai shafi abokan hulda da ke kan tsarin 'band B, C, D, da E' ba.

Kara karanta wannan

Kano: KEDCO ya yanke wutar lantarkin jami'ar Dangote saboda taurin bashi

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa karin ya biyo bayan amincewar hukumar NERC na yin karin kudin wuta ga 'yan tsarin 'band A' a wata wata gwargwadon sauye-sauyen ma'aunin tattalin arziki.

Ma'aunan da ake dubawa wajen karin kudin wutar sun hada da sauyi a farashin canjin kudade na kasashen waje, hauhawar farashin kayayyaki da karuwar farashin gas.

Hukumar NERC ta yi karin kudin wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnati ta yi karin haske kan dalilin da ya sa ta yi karin kudin wutar lantarkin sama da 200% ga 'yan tsarin 'band A'.

A wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, mataimakin shugaban NERC, Musliu Oseni, ya ce an kara kudin daga N66/KwH zuwa N225/KwH.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.