Shugaban EFCC Ya Koka Kan Girman Satar da Ake Yi, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi

Shugaban EFCC Ya Koka Kan Girman Satar da Ake Yi, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi

  • Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da masu aikata rashin gaskiya ya koka kan irin girman satar da ake yi a ƙasar nan
  • Ola Olukoyede ya bayyana cewa wasu lokutan yana mamakin yadda ƙasar nan har yanzu ba ta ruguje ba saboda barnar
  • Shugaban hukumar tarayyar ya ce idan ya yi arba da wasu takardun shari'a kan satar da aka yi, abin na tada masa hankali
  • Shugaban na EFCC ya kuma ƙara da cewa da ƴan Najeriya za su ga irin girman satar da ake yi, da dole sai sun zubar da ƙwalla

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, Ola Olukoyede, ya koka kan girman satar da wasu masu cin hanci da rashawa ke yi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan jami'in hukumar EFCC ya salwantar da ransa

Ya bayyana cewa ya kan kasance a cikin mamaki kan yadda har yanzu ƙasar nan ba ta durƙushe ba duk lokacin da ya duba takardun shari'a ya ga irin kuɗaɗen da aka sata.

Shugaban EFCC ya koka kan cin hanci a Najeriya
Shugaban EFCC ya koka kan satar da ake yi a Najeriya Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Facebook

Ola Olukoyede ya ƙara da cewa da ƴan Najeriya za su ga wasu daga cikin takardun shari'ar da sun zubar da ƙwalla.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sugahban EFCC a kan sata a Najeriya

A cewar wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Talata a shafin X, shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin hukumar RMAFC.

"A lokacin da na duba wasu takardun shari'a na ga irin maƙudan kuɗin da aka sace, ina mamakin yadda har yanzu ƙasar nan take a tsaye. Idan ka ga wasu takardun dole a zubar da ƙwalla."

Kara karanta wannan

Harin bam a Borno: Majalisa ta bayyana wurin da 'yan ta'addan suka fito

"Za ka rasa wane irin hali mu ƴan Najeriya muke da shi duba da yadda suke tura ragowar kuɗin kasafin kuɗi da ba a kashe ba zuwa asusun banki kafin tsakar dare a ƙarshen kasafin kuɗi."

- Ola Olukoyede

Hukumar EFCC ta fadi mafi girman cin hanci

Ya kuma bayyana cewa cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikatan gwamnati shi ne mafi girman cin hanci a Najeriya.

Ya yi nuni da cewa idan aka kawar da cin hanci a ɓangaren gwamnati, ƙasar nan za ta yiwa ƙasashen duniya masu yawa fintinkau wajen ci gaba.

Jami'in EFCC ya kashe kansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami’in hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ya yanke shawarar barin duniya.

Jami'in na hukumar EFCC ya salwantar da ransa ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng