'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 4 a Wani Hari a Jihar Katsina

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 4 a Wani Hari a Jihar Katsina

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun aikata sabon ta'addanci a jihar Katsina bayan sun farmaki wasu manoma suna tsaka da aiki a gonakinsu
  • Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a ƙaramar hukumar Jibia sun hallaka mutum huɗu waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Kashe manoman na zuwa ne bayan ƴan bindiga sun hallaka jami'an ƴan sanda mutum biyar a wani kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun hallaka wasu manoma mutum huɗu yayin da suke aiki a gonakinsu a jihar Katsina.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutanen ne a ƙaramar hukumar Jibia mai fama da matsalar rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutum 116 sun rasu a wurin taron addini

'Yan bindiga sun hallaka mutum hudu a Katsina
'Yan bindiga sun hallaka manoma a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Katsina

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Gurbin Magarya da Zaure na yankin Kukar Babangida a ƙaramar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da aka kashe mutum uku a Gurbin Magarya, an kashe mutum na huɗun ne a Zaure da ke yankin Kukar Babangida.

Wata majiya wacce ta koka kan aukuwar lamarin, ta yi kira ga mazauna yankin da su haɗa kai da jami'an tsaro domin shawo kan matsalar rashin tsaron.

Miyagun Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sanda

Harin na zuwa ne bayan ƴan bindiga sun kashe jami'an ƴan sanda biyar tare da raunata wani ɗaya a ƙaramar hukumar ta Jibia.

Jami'an ƴan sandan dai na tafiya ne daga sansaninsu da ke ƙauyen Zandam zuwa Jibia lokacin da ƴan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi nasarar dakile harin 'yan bindiga sun ceto mutum 10

Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi mataimakin shugaban kwamitin tsaro na Jibia, Malam Nasiru Jibia, ya bayyana cewa mutum ɗaya ne kawai aka kashe a Gurbin Magarya a ranar Litinin.

Ya kuma tabbatar da kisan da aka yiwa jami'an ƴan sandan a ranar Lahadi bayan an yi musu kwanton ɓauna.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, bai ɗauki kiran da aka yi masa a waya ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutum ɗaya ya mutu, sannan an ceto wasu mutum 10 bayan ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Harin ya auku ne lokacin da ƴan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari a wani gida da ke bayan unguwar Comprehensive Quarters a ƙaramar hukumar Dutsinma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel