Sarkin Musulmi a Shirye Yake, Zai Karɓi Kowacce Dokar Gwamnatin Sokoto
- Sarkin Musulmin Najeriya, mai martaba Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, yace zai yi biyayya ga gwamnatin jihar Sokoto
- MA yayin kammala taron jin ra'ayin jama'a kan sabunta dokar masarautarsa, mai martaba ya c zai bi duk abin da dokar ta tanadar
- Tun da fari, Antoni Janar na jihar Sokoto ya ce gwamnan jihar ce ke da wuƙa da nama wurin naɗin sarauta da bada aiki a masarautar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana shirinsa da burinsa na karɓar kowacce doka da gwamnatin jihar Sokoto za ta gindaya.
Jagoran Musulmin Najeriya, ya bayyana hakan a ranar Talata a ƙaramin zauren majalisar jihar Sokoto yayin kammala jin ta bakin jama'a kan gyaran dokar kananan hukumomin jihar.
Dakta Jabbi Kilgori, mamba a majalisar masarautar Sokoto kuma mai daya daga cikin masu naɗin sarakuna ne ya wakilci sarkin musulmi, rahoton Vanguard ya bayyana
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan dokar ta tsallake, za a janyewa Sarkin Musulmin duk wani ƙarfin ikonsa na naɗi ko tuɓe kowanne basaraken gargagjiya a jihar.
Gwamnatin Sokoto ta yi bayanin doka
Jaridar The Nation ta ruwaito Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Nasiru Mohammed Binji ya yi bayani kan matsayin nadin sarauta a dokance.
Mista Nasiru ya ce ikon naɗa hakimai da sauran sarautu yana wurin gwamnati bisa bisa la'akari da sashi na 5, ƙaramin sashi na 2 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana ƙarara cewa naɗa hakimai ko dagatai yana wurin masu mulki kuma gwamna ne mutum ɗaya da ke da wannan ikon a jihar.
Binji ya bayyana cewa, sabuwar dokar idan aka yi mata kwaskwarima za ta inganta lamurran ƙaramar hukuma da masarautu.
Gaskiyar rikicin Sarkin Musulmi da Gwamna
A wani labari na daban, fadar sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad III ta ce babu wata ɓaraka tsakaninta da gwamnatin jihar Sokoto ba kamar yadda ake yadawa ba.
Fadar ta sanar da cewa, ita mai biyayya ce duk wata doka da gwamnatin jihar zata saka ba tare da ta bijire ba, yayin da take magana kan batun janye karfin ikon sarkin Musulmi.
Asali: Legit.ng