SSANU: Kungiyar Ma'aikata Za Su Tafi Yajin Aiki, An Fadi Ranar da Za a Rufe Jami’o’i

SSANU: Kungiyar Ma'aikata Za Su Tafi Yajin Aiki, An Fadi Ranar da Za a Rufe Jami’o’i

  • Kungiyar manyan ma'aikatan jami'a ta kasa (SSANU) ta yi barazanar rufe dukkan jami'o'in Najeriya cikin makon da muke ciki
  • Kungiyar SSANU za ta dauki matakin ne bayan gwamnatin tarayya ta gaza nuna alamar cika alkawarin da suka rattabawa hannu
  • A kwanakin baya ne kungiyar SSANU ta ba gwamantin tarayya wa'adin mako biyu domin biya mata bukata amma har yanzu shiru

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar manyan ma'aikatan jami'a ta kasa (SSANU) ta yi barazanar rufe dukkan jami'o'in Najeriya.

Hakan ya biyo bayan cikar wa'adin mako biyu da kungiyar ta ba gwamantin tarayya ne domin biya mata bukatunta.

Kara karanta wannan

NIN: Majalisar dattawa na kokarin kawo dokar da za ta shafi yan ƙasashen waje

Kungiyar SSANU
Kungiyar SSANU za ta shiga yajin aiki. Hoto: Majority World
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar SSANU ta dauki matakin ne bayan wani taro da ta yi a ranar Talata a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe SSANU za ta rufe jami'o'i?

Kungiyar SSANU ta bayyana cewa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli za ta kulle dukkan jami'o'in Najeriya, rahoton Leadership.

Dama tun a zama na 48 da kungiyar ta yi a jami'ar Edo da ke Benin ta bayyana cewa da zarar mako biyu sun cika gwamanti ba ta dauki mataki ba, za ta tafi yajin aiki.

A kan menene SSANU za ta rufe jami'o'i?

SSANU za ta rufe jami'o'i ne a kan rashin biyan 'yan kungiyar albashin da gwamnatin tarayya ta rike musu na watanni hudu.

Tun a dogon yajin aikin da kungiyoyin ma'aikatan jami'a suka yi a shekarar 2022 suke bin gwamantin tarayya bashi amma kudin sun gagara fitowa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji yan bindiga a jihohi, sun kama manyan 'yan ta'adda

SSANU: 'Ya kamata a rika cika alkawari'

Kungiyar SSANU ta ce abin Allah wadai ne yadda gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawarin da ta rattabawa hannu.

Kungiyar ta ce anyi alkawari da ministan ilimi, ministan kwadago har ma da majalisar dokokin Najeriya amma har yau an gaza cika alkawarin.

Dalibi ya mutu a jami'ar FUOYE

A wani rahoton, kun ji cewa jami’ar gwamnatin tarayya, da ke Oye-Ekiti, (FUOYE) ta zargi ƴan ƙungiyar SSANU/NASU da kasancewa silar mutuwar wani ɗalibin makarantar.

Rahotanni sun nuna cewa mahukuntan FUOYE sun ce ɗalibin wanda yake fama da ciwon asma ya mutu ne saboda an kulle asibitin jami'ar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel