'Yan Sanda Sun Yi Nasarar Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 10

'Yan Sanda Sun Yi Nasarar Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 10

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarar daƙile harin da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Dutsinma
  • Ƴan sandan sun yi nasarar ceto mutum 10 da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su a harin da suka kai ranar Talata
  • A yayin harin dai miyagun ƴan bindigan sun sace mutum 14 tare da hallaka wani mutum ɗaya bayan sun harbe shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Aƙalla mutum ɗaya ya mutu, sannan an ceto wasu mutum 10 bayan ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Harin ya auku ne a ranar Talata lokacin da ƴan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari a wani gida da ke bayan unguwar Comprehensive Quarters a ƙaramar hukumar Dutsinma.

Kara karanta wannan

Harin bam a Borno: Majalisa ta bayyana wurin da 'yan ta'addan suka fito

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga tare da ceto mutum 10 a Katsina Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A yayin harin, an ce ƴan bindigan sun harbe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da mutane kusan 14, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An garzaya da wanda ya samu raunuka zuwa asibiti domin kula da lafiyarsa inda daga bisani kuma aka tabbatar da mutuwarsa.

Me ƴan sandan Katsina suka ce kan harin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, a wata sanarwa ya bayyana cewa, bayan samun rahoton, ƴan sanda a Dutsinma sun garzaya wurin inda suka yi artabu da masu garkuwa da mutanen.

"Tawagar ta yi nasarar daƙile harin tare da ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su. Za a ci gaba da bayar da ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike."

- ASP Abubakar Sadiq

Jaridar TheCable ta ce sanarwar ta ƙara da cewa kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina, Aliyu Musa, ya tura tawaga zuwa dazuzzukan da ke makwabtaka da wajen domin ceto waɗanda aka sace tare da cafke ƴan bindigan.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a wani samame a jihar Benue

Ƴan sanda sun hallaka ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Benue sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga mutum biyu yayin wani samame da suka kai.

Ƴan sandan sun samu nasarar ne bayan da suka kai hari a sansanin ƴan bindigan da ke a gundumar Mbatyula cikin ƙaramar hukumar Katsina-Ala a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng