Nnamdi Kanu: Gwamnonin Kudu Maso Gabas Sun Fadi Matsayarsu Kan Sakin Shugaban IPOB
- Ƙungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Gabas sun gana a jihar Enugu domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yankin na su
- Gwamnonin a yayin ganawar ta su sun cimma matsayar za su gana da shugaban ƙasa kan ƙalubalen matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin
- Sun kuma yanke shawarar cewa za su buƙaci a saki shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu wanda ke fuskantar tuhumar ta'addanci a gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Ƙungiyar gwamnonin Kudu Maso Gabas ta ƙudiri aniyar ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ƙungiyar za ta gana da shugaban ƙasan ne domin neman a sako shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu.
Jaridar Premium Times ta ce gwamnonin jihohin Imo (Hope Uzodinma), Ebonyi (Francis Nwifuru) da Abia (Alex Otti) sun hadu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Anambra (Charles Soludo) da takwaransu na jihar Enugu, Peter Mbah, sun yi ganawar sirrin a Enugu ranar Talata.
Kanu: Wace matsaya gwamnonin suka cimma?
A cikin sanarwar da suka fitar a ƙarshen taron, ƙungiyar gwamnonin ta ce sun yanke shawarar neman a sako shugaban ƙungiyar ta IPOB, rahoton jaridar Leadership ta tabbatar.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda ya karanta wa manema labarai sanarwar, ya ce ƙungiyar ta kuma ƙuduri aniyar magance matsalar rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas.
"Ƙungiyar ta amince za ta gana da shugaban ƙasa domin tattaunawa kan matsalolin da suka shafi yankin Kudu maso Gabas."
"Ƙungiyar ta kuma tattauna tare da amincewa da zama da gwamnatin tarayya domin neman a sako Mazi Nnamdi Kanu."
- Hope Uzodinma
Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar tuhumar ta’addanci a babbar kotun tarayya da ke Abuja, yana tsare tun bayan da aka sake kama shi a watan Yunin 2021.
Kotu ta yi watsi da ƙarar Nnamdi Kanu
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta yi fatali da ƙarar da shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya shigar a gabanta.
Nnamdi Kanu, ta bakin lauyoyinsa ya shigar da gwamnatin tarayya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ƙara a gaban kotun ya na neman a biya shi diyyar N1bn.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng