'Yan Sanda Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Wani Samame a Jihar Benue

'Yan Sanda Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Wani Samame a Jihar Benue

  • Wasu miyagun ƴan bindiga a jihar Benue sun gamu da ajalinsu bayan sun fafata da jami'an ƴan sanda a cikin daji
  • Jami'an ƴan sandan dai sun kai farmaki ne a sansanin ƴan bindigan inda suka hallaka mutum biyu daga cikinsu bayan sun yi musayar wuta
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da hakan ta ƙara da cewa an ƙwato kayayyaki masu yawa daga sansanin ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Benue sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga mutum biyu.

Ƴan sandan sun samu nasarar ne bayan da suka kai hari a sansanin ƴan bindigan da ke a gundumar Mbatyula cikin ƙaramar hukumar Katsina-Ala a jihar.

Kara karanta wannan

Harin bam a Borno: Majalisa ta bayyana wurin da 'yan ta'addan suka fito

'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga a Benue
'Yan sun yi galaba kan 'yan bindiga a Benue Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun yi nasara kan ƴan bindiga

Catherine ta ce an samu nasarar ne sakamakon ci gaba da ƙoƙarin da ƴan sanda ke yi na murƙushe ƴan bindiga a yankin Sankera na jihar cikin watanni uku da suka gabata, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

"Jami'an ƴan sanda na Operation Zenda JTF sun farmaki maɓoyar ƴan bindiga a ƙauyen Tse Uza, da ke gundumar Mbatyula a ƙaramar hukumar Katsina-Ala a ranar Lahadi, 30 ga watan Yunin 2024."
"Bayan sun isa sansanin, ƴan bindiga sun buɗe musu domin hana su shiga amma ƴan sandan sun ci ƙarfinsu."
"Likita ya tabbatar da mutuwar biyu daga cikin ƴan bindigan da suka samu raunuka, sannan an ajiye gawarwakinsu a babban asibitin Ukum yayin da sauran waɗanda ake zargi suka tsere."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yiwa jami'an tsaro kwantan ɓauna, an rasa rayuka a Katsina

- Catherine Anene

An karbo kaya a hannun 'yan bindiga

Catherene Anene ta ce kayayyakin da aka ƙwato daga sansanin sun haɗa da ƙananan bindigu guda biyu cike da harsasai, bindigu ƙirar gida guda uku.

Sannan an samu babura guda 13, mota ƙirar Toyota Corolla guda ɗaya da keke mai ƙafa uku guda ɗaya

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki kan jami'an tsaro a shingen binciken ababen hawa a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun buɗe wuta tare da halaka jami'an ƴan sanda biyu a harin da suka shingen bincike da ke garin Aba a jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng