Rikicin Masarauta: Sarki Aminu Ado Bayero Bai Gamsu ba, Ya Roki a Canza Alkaliya a Kotu
- Lauyoyin sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun zargi cewa kotu ba za ta yiwa wanda su ke wakilta adalci ba saboda wasu zarge-zarge
- Lauyan sarkin, Barista AbdulRazaq Ahmad ya roki mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta tsame kanta daga ci gaba da gudanar da shari'ar
- Lauyoyin na ganin tun lokacin da mai shari'a ta dakatar da sarki Aminu Bayero daga bayyana kansa a matsayin sarki su ke zargin da matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- A yau Talata kotu a Kano ta ci gaba da sauraron dambarwar masarautar Kano, inda bangaren da ke kare sarki na 15, Aminu Ado aBayero ya zargi kotu da bangaranci.
Daya daga lauyoyin sarkin, Barista Abdulrrazak Ahmad ya roki alkaliyar kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu da ta tsame kanta daga ci gaba da sauraron karar.
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa suna rokon mai shari'ar ta daina sauraren karar saboda zargin ba za a yi masu adalci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsoron Lauyoyin Aminu Ado Bayero
Lauyoyin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun zargi mai sauraron shari'ar dambarwar masarauta da cewa ta riga ta yanke hukunci kafin ta saurari karar.
Barista Abdulrazak Ahmad ya kara da cewa, tun gabanin fara shari'ar kotun ta haramta wa Alhaji Aminu Ado Bayero kiran kansa Sarkin Kano, kamar yadda DailyNews24 ta wallafa.
Martanin gwamnatin Kano a shari'ar masarauta
A nasa bangaren, lauyan gwamnati Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci ya bayyana mamakinsa ga yadda lauyan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya zargi alkaliyar da nuna bangaranci.
Gwamnatin Kano ce ta shigar da kara kotun ta na neman a hana sarki Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna da ci gaba da bayyana kansu a matsayin sarakuna a jihar.
Kotu ta dauki mataki kan rikicin masarauta
A wani labarin kun ji cewa babbar kotu da ke zamanta a Kano ta dauki mataki kan rikicin masarauta da ake ci gaba da yi a jihar.
Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta dage sauraron shari'ar bayan sauraron bangarorin biyu, za a ci gaba da zama a ranar 4 Yuli, 2024 domin bayyana matsayar kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng