Bayan Shafe Shekaru 15 a Gidan Yari, Kotu Ta Saki Wani Mutum Ba Tare da Shari'a Ba

Bayan Shafe Shekaru 15 a Gidan Yari, Kotu Ta Saki Wani Mutum Ba Tare da Shari'a Ba

  • Babbar kotun jiha ta Legas ta saki wani mutum daga gidan yari bayan ya shafe shekaru 15 a tsare
  • An gano cewa tsawon shekarun nan yana garƙame a gidan yarin Kirikiri ba tare da an taba gurfanar da shi ba
  • Lauyan mutumin ya buƙaci kotu ta ayyana abin da aka yi da rashin daidai, rashin adalci da kuma take haƙkin ɗan Adam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - A ranar Litini ne babbar kotun jihar Legas da ke Ikeja, ta ba da umarni a saki wani mutum mai suna Kazeen Adeshina, bayan kwashe shekaru 15 a gidan yari ba tare da an yi shari'arsa ba.

Kara karanta wannan

Gini ya rufta kan mutane 2 a Abuja, gwamnati ta dauki matakin gaggawa

Mai shari'a Oyindamola Ogala, ya bayar da umarnin sakin mutumin a wani hukunci da ya yanke kan ƙarar take hakkinsa na ɗan Adam da aka yi ta hannun lauyansa Ben Okeke.

Kotu ta saki mutumin da aka tsare shekaru 15 a gidan yarin Legas
Kotu ta yi hukunci kan mutumin da aka tsare shekaru 15 ba tare da tuhuma ba. Hoto: Federal High Court
Asali: UGC

Premium Times ta bayyana cewa, alƙalin ya ce ajiye Adeshina a gidan yari ba tare da laifi ko shari'a ba rashin adalci ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yanke hukunci kan tsare Adeshina

Mista Ogala ya ce babu adalci a kama Adeshina da cigaba da tsare shi da aka yi a gidan gyaran hali na Kirikiri da ke Legas ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Bayan duba shari'ar Adeshina, alƙalin ya bayar da umarnin sakin Adeshina nan take kuma ba tare da cika wasu sharuɗɗa ba, kamar yadda jaridar Guardian ta bayyana.

An maka gwamnatin Legas a kotu

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta mayar da martani kan ɗaga tuta a fadar da Aminu Ado ke zaune

A ruwayar Vanguard, Lauyan Adeshina, Mista Okeke, ya yi karar Antoni Janar na Legas, kwamishinan 'yan sanda, shugaban hukumar gidan gyaran hali da gwamnatin Legas.

Mista Okeke ya roki kotun da ta bi wa wanda yake karewa kadin tauye hakkinsa na dan Adam da aka yi sakamakon tsare shi na tsawon shekaru 15 ba tare da shari'a ba.

Ministan Tinubu da rigar N3m

A wani labari na daban, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya saka rigar Naira miliyan uku inda ya halarci wani taro.

Cike da fushin halin da talakawa suke ciki, 'yan Najeriya sun yi masa tatas bayan bayyanarsa da rigar mai nuna aji da isa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel